|
| 1 |
|
| Sai Ayuba ya amsa, |
|
| 2 |
|
| “Lalle, na san wannan gaskiya ne. Amma ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah? |
|
| 3 |
|
| Ko da mutum yana so yă yi gardama da shi, ba zai taɓa amsa masa ba ko da sau ɗaya cikin dubu. |
|
| 4 |
|
| Hikimarsa tana da zurfi, ikonsa yana da yawa. Wane ne ya taɓa yin faɗa da shi har ya yi nasara? |
|
| 5 |
|
| Yana matsar da manyan duwatsu kafin su sani kuma yana juya su cikin fushinsa. |
|
| 6 |
|
| Yana girgiza ƙasa, yana girgiza harsashenta. |
|
| 7 |
|
| Yana magana da rana sai ta ƙi yin haske; yana hana taurari yin haske. |
|
| 8 |
|
| Shi kaɗai ya shimfiɗa sammai ya kuma yi tafiya a kan raƙuman ruwan teku. |
|
| 9 |
|
| Shi ne ya halicci Mafarauci da Kare da Zomo, da Kaza, da ’Ya’yanta da tarin taurari a sama, da taurarin kudu. |
|
| 10 |
|
| Yana yin abubuwan banmamaki waɗanda ba a iya ganewa, mu’ujizai waɗanda ba a iya ƙirgawa. |
|
| 11 |
|
| Ba na iya ganinsa lokacin da ya wuce ni; ba na sani ya wuce lokacin da ya wuce. |
|
| 12 |
|
| Wane ne ya isa yă hana shi in ya ƙwace abu? Wa zai ce masa, ‘Me kake yi?’ |
|
| 13 |
|
| Allah ba ya danne fushinsa; ko dodannin ruwan da ake kira ayarin Rahab ya tattake su. |
|
| 14 |
|
| “Ta yaya zan iya yin faɗa da shi? Ina zan iya samun kalmomin da zan yi gardama da shi? |
|
| 15 |
|
| Ko da yake ba ni da laifi, ba zan iya amsa masa ba; sai dai roƙon jinƙai zan iya yi ga mahukuncina. |
|
| 16 |
|
| Ko da na yi kira gare shi ya amsa mini, ban yarda cewa zai saurare ni ba. |
|
| 17 |
|
| Zai sa hadari yă danne ni yă ƙara mini ciwona ba dalili. |
|
| 18 |
|
| Ba zai bari in yi numfashi ba, sai dai yă ƙara mini azaba. |
|
| 19 |
|
| In maganar ƙarfi ne, shi babban mai ƙarfi ne! In kuma maganar shari’a ne, wa zai kai kararsa? |
|
| 20 |
|
| Ko da ni marar ƙarfi ne, bakina ya isa yă sa in zama mai laifi; in ba ni da laifi, zai sa in yi laifi. |
|
| 21 |
|
| “Ko da yake ba ni da laifi, ban damu da kaina ba; na rena raina. |
|
| 22 |
|
| Ba bambanci; shi ya sa na ce, ‘Yana hallaka marasa laifi da kuma mugaye.’ |
|
| 23 |
|
| Lokacin da bala’i ya kawo ga mutuwa, yakan yi dariyar baƙin cikin marasa laifi. |
|
| 24 |
|
| Lokacin da ƙasa ta faɗa a hannun mugaye, yakan rufe idanun masu shari’a. In ba shi ba wa zai yi wannan? |
|
| 25 |
|
| “Kwanakina sun fi mai gudu wucewa da sauri; suna firiya babu wani abin jin daɗi a cikinsu. |
|
| 26 |
|
| Suna wucewa kamar jirgin ruwan da aka yi da kyauro, kamar jahurma da ta kai wa namanta cafka. |
|
| 27 |
|
| ‘In na ce zan manta da abin da yake damu na, zan yi murmushi in daina nuna ɓacin rai,’ |
|
| 28 |
|
| duk da haka ina tsoron duk wahalata, domin na san ba za ka ɗauke ni marar laifi ba. |
|
| 29 |
|
| Tun da an riga an ɗauke ni mai laifi, duk ƙoƙarina a banza yake. |
|
| 30 |
|
| Ko da na wanke jikina duka da sabulu, na wanke hannuwana kuma da soda, |
|
| 31 |
|
| duk da haka za ka jefa ni cikin ƙazamin wuri, yadda ko rigunan jikina ma za su ƙi ni. |
|
| 32 |
|
| “Shi ba mutum ba ne kamar ni wanda zan iya amsa masa, har da za mu yi faɗa da juna a wurin shari’a. |
|
| 33 |
|
| In da akwai wanda zai iya shiga tsakaninmu, ya ɗora hannunsa a kanmu tare, |
|
| 34 |
|
| wani wanda zai sa Allah yă daina duka na, don yă daina ba ni tsoro. |
|
| 35 |
|
| Sa’an nan ne zan iya yin magana ba tare da jin tsoronsa ba, amma a yadda nake a yanzu ba zan iya ba. |
|
|
|
|