×

Littafi Mai Tsarki 1979

Zabura 101

1
Waƙata ta aminci ce da gaskiya. Ina raira maka ita, ya Ubangiji.
2
Abin da nake yi ba zai zama laifi ba, Yaushe za ka zo wurina? Da zuciya mai tsabta zan zauna a gidana.
3
Ba zan jure da mugunta ba ko kaɗan. Na ƙi jinin ayyukan waɗanda suka bijire wa Allah, Ba ruwana da su.
4
Ba zan yi rashin aminci ba, Ba kuwa zan yi tunanin mugunta ba.
5
Zan hallakar da mai raɗar abokinsa, Ba zan jure da mutum mai girmankai, Ko mai alfarma ba.
6
Zan yarda da waɗanda suke amincewa da Allah, Zan yardar musu si yi zamansu a fādata, Zan yarda wa waɗanda suke da tabbataccen aminci Su yi mini hidima.
7
Maƙaryaci ba zai zauna a fādata ba, Ba zan yarda munafuki ya yi zamansa a wurina ba.
8
A kowace rana zan yi ta karkashe dukan mugayen da suke cikin ƙasarmu, Zan kori dukan mugaye daga birnin Ubangiji.
Hausa Bible 1979
@ Bible Society of Nigeria 1979
:
Adana Bayanan kula