Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Ubangiji ya ce wa Mai Girma, Sarkina, “Zauna nan a damana, Har in sa maƙiyanka a ƙarƙashin sawayenka.” |
| 2 |
| Tun daga Sihiyona Ubangiji zai faɗaɗa sarautarka, ya ce, “Ka yi mulki bisa maƙiyanka.” |
| 3 |
| A ranar da za ka yi yaƙi da maƙiyanka, Jama'arka za su kawo maka gudunmawa don kansu. Kamar yadda raɓa take da sassafe, Haka samarinka za su zo wurinka a tsarkakan tsaunuka. |
| 4 |
| Ubangiji ya yi muhimmin alkawari, Ba kuwa zai fasa ba! “Za ka zama firist har abada Bisa ga tsabi'ar Malkisadik firist.” |
| 5 |
| Ubangiji yana damanka, Zai kori sarakuna a ranar da ya husata. |
| 6 |
| Zai shara'anta wa dukan sauran al'umma, Ya rufe fagen fama da gawawwaki, Zai kori sarakunan duk duniya. |
| 7 |
| Sarkin zai sha ruwan rafin da yake kan hanya, Ya wartsake ya sami ƙarfi. Zai yi tsayawar nasara. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/psalms/110.mp3
150
110