Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Mai farin ciki ne mutumin da yake tsoron Ubangiji, Mai farin ciki ne shi wanda yake jin daɗin yin biyayya da umarnansa. |
| 2 |
| 'Ya'yansa za su zama manyan ƙasar, Zuriyar mutumin kirki za ta yi albarka. |
| 3 |
| Iyalinsa za su zama attajirai masu dukiya, Adalcinsa zai tabbata har abada. |
| 4 |
| Haske yakan haskaka wa mutanen kirki a cikin duhu, Da waɗanda suke yin alheri, da jinƙai, da gaskiya. |
| 5 |
| Mai farin ciki ne mutumin da yakan ba da rance hannu sake, Wato wanda yake yin harkarsa da gaskiya. |
| 6 |
| Mutumin kirki ba zai kāsa ba daɗai, Ba za a taɓa mantawa da shi ba. |
| 7 |
| Ba ya tsoron jin mugun labari, Bangaskiyarsa tana da ƙarfi, Ga Ubangiji yake dogara. |
| 8 |
| Ba shi da damuwa ko tsoro, Ya tabbata zai ga faɗuwar maƙiyansa. |
| 9 |
| Yakan bayar ga matalauta hannu sake, Alherinsa kuwa dawwamamme ne. Zai zama mai iko wanda ake girmamawa. |
| 10 |
| Sa'ad da mugaye suka ga wannan, Sai suka tunzura, suka harare shi da fushi, suka ɓace, Sa zuciyarsu ta ƙare har abada. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/psalms/112.mp3
150
112