Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Yabi Ubangiji. Mai albarka ne mutumin da yake tsoron Ubangiji, wanda yakan sami farin ciki mai girma a umarnansa. |
| 2 |
| ’Ya’yansa za su zama manya a ƙasar; tsaran masu aikata gaskiya za su sami albarka. |
| 3 |
| Wadata da arziki suna a cikin gidansa, adalcinsa zai dawwama har abada. |
| 4 |
| Ko a cikin duhu haske kan haskaka wa mai aikata gaskiya, mai alheri mai tausayi da kuma mai adalci. |
| 5 |
| Abu mai kyau zai zo masa shi da yake kyauta yake kuma ba da bashi hannu sake, shi da yake yin al’amuransa cikin gaskiya. |
| 6 |
| Tabbatacce ba zai taɓa jijjigu ba; za a tuna da mai adalci har abada. |
| 7 |
| Ba zai ji tsoron labari marar daɗi ba; zuciyarsa tsayayyiya ce, tana dogara ga Ubangiji. |
| 8 |
| Zuciyarsa tana da kāriya, ba zai ji tsoro ba; a ƙarshe zai zama mai nasara a kan maƙiyansa. |
| 9 |
| Ya rarraba kyautansa ga matalauta, adalcinsa zai dawwama har abada; za a ɗaga ƙahonsa sama da bangirma. |
| 10 |
| Mugun mutum zai gani yă kuma yi fushi, zai ciza haƙora yă kuma lalace; sha’awace-sha’awacen mugaye za su zo ga ƙarshe. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/112.mp3
150
112