Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Da a ce Ubangiji ba ya tare da mu, Da me zai faru? Ba da amsa, ya Isra'ila! |
| 2 |
| “Da a ce Ubangiji ba ya tare da mu, A lokacin da abokan gābanmu suka auka mana, |
| 3 |
| Da sun haɗiye mu da rai a lokacin nan, Saboda zafin fushi da suke yi da mu, |
| 4 |
| Da rigyawa ta kwashe mu, Da ruwa yi ci mu, |
| 5 |
| Kwararowar ruwa ya nutsar da mu.” |
| 6 |
| Sai mu gode wa Ubangiji, Da bai bar abokan gābanmu su hallaka mu ba. |
| 7 |
| Mun kuɓuta kamar tsuntsu daga tarkon mai farauta, Tarkon ya tsinke, mun 'yantu! |
| 8 |
| Taimakonmu daga wurin Ubangiji yake zuwa, Shi wanda ya yi sama da duniya. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/psalms/124.mp3
150
124