|
| 1 |
|
| Ku gode wa Ubangiji domin shi mai alheri ne, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 2 |
|
| Ku gode wa Allahn da ya fi dukan alloli girma, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 3 |
|
| Ku gode wa Ubangijin dukan iyayengiji, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 4 |
|
| Shi kaɗai ne yake aikata mu'ujizai masu girma, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 5 |
|
| Ta wurin hikimarsa ya halicci sammai, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 6 |
|
| Ya kafa duniya a bisa kan ruwa mai zurfi, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 7 |
|
| Shi ne ya halicci rana da wata, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce, |
|
| 8 |
|
| Rana don ta yi mulkin yini, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce, |
|
| 9 |
|
| Wata da taurari kuwa don su yi mulkin dare, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 10 |
|
| Shi ya karkashe 'ya'yan fari maza, na Masarawa, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 11 |
|
| Shi ya fito da jama'ar Isra'ila daga cikin Masar, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 12 |
|
| Da ƙarfinsa da ikonsa ya fito da su, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 13 |
|
| Shi ne ya keta Bahar Maliya biyu, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 14 |
|
| Shi ya bi da jama'arsa ta cikin tekun, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 15 |
|
| Shi ne ya sa ruwa ya ci Fir'auna da rundunarsa, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 16 |
|
| Ya bi da jama'arsa cikin hamada, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 17 |
|
| Ya karkashe sarakuna masu iko, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 18 |
|
| Ya karkashe shahararrun sarakuna, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 19 |
|
| Ya kashe Sihon, Sarkin Amoriyawa, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 20 |
|
| Ya kashe Og, Sarkin Bashan, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 21 |
|
| Ya ba da ƙasarsu ga jama'arsa, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 22 |
|
| Ya ba da ita ga bawansa Isra'ila, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 23 |
|
| Bai manta da mu sa'ad da aka yi nasara da mu ba, Gama ƙaunarsa madawwamiyar ce. |
|
| 24 |
|
| Ya 'yantar da mu daga abokan gābanmu, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 25 |
|
| Yana ba da abinci ga dukan mutane da dabbobi, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 26 |
|
| Ku yi wa Allah sa Sama godiya, Gama ƙaunarsa madawwamiyar ce. |
|
|
|
|