|
| 1 |
|
| Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi. Ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 2 |
|
| Ku yi godiya ga Allahn alloli. Ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 3 |
|
| Ku yi godiya ga Ubangijin iyayengiji. Ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 4 |
|
| Gare shi wanda shi kaɗai yake aikata abubuwan banmamaki, Ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 5 |
|
| Wanda ta wurin ganewarsa ya yi sammai, Ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 6 |
|
| Wanda ya shimfiɗa duniya a kan ruwaye, Ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 7 |
|
| Wanda ya yi manyan haskoki, Ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 8 |
|
| Rana don tă yi mulkin yini, Ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 9 |
|
| Wata da taurari kuma don su yi mulkin dare; Ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 10 |
|
| Gare shi wanda ya kashe ’ya’yan fari Masar Ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 11 |
|
| Ya kuma fitar da Isra’ila daga cikinsu Ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 12 |
|
| Da hannu mai ƙarfi da hannu mai iko; Ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 13 |
|
| Gare shi wanda ya raba Jan Teku biyu Ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 14 |
|
| Ya kawo Isra’ila ta tsakiyarsa, Ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 15 |
|
| Amma ya share Fir’auna da mayaƙansa cikin Jan Teku; Ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 16 |
|
| Gare shi wanda ya bi da mutanensa cikin hamada, Ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 17 |
|
| Wanda ya buge manyan sarakuna, Ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 18 |
|
| Ya karkashe manyan sarakuna, Ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 19 |
|
| Sihon sarkin Amoriyawa Ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 20 |
|
| Da kuma Og sarkin Bashan, Ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 21 |
|
| Ya kuma ba da ƙasarsu gādo, Ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 22 |
|
| Gādo ga bawansa Isra’ila; Ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 23 |
|
| Shi wanda ya tuna da mu cikin ƙasƙancinmu Ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 24 |
|
| Ya kuma ’yantar da mu daga abokan gābanmu, Ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 25 |
|
| Wanda kuma ke ba da abinci ga kowace halitta. Ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
| 26 |
|
| Ku yi godiya ga Allah na sama. Ƙaunarsa madawwamiya ce. |
|
|
|
|