Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| A bakin kogunan Babilon muka zauna muka yi kuka sa’ad da muka tuna da Sihiyona. |
| 2 |
| A can a kan rassan itatuwa muka rataye garayunmu, |
| 3 |
| gama a can masu kamunmu suka sa mu yi waƙoƙi, masu ba mu azaba suka nema waƙoƙin farin ciki; suka ce, “Ku rera mana ɗaya daga cikin waƙoƙin Sihiyona!” |
| 4 |
| Yaya za mu rera waƙoƙin Ubangiji a baƙuwar ƙasa? |
| 5 |
| In na manta da ke, ya Urushalima, bari hannuna na dama manta da iyawarsa. |
| 6 |
| Bari harshena yă manne wa rufin bakina in ban tuna da ke ba, in ban so Urushalima farin cikin mafi girma ba. |
| 7 |
| Ka tuna, ya Ubangiji, abin da mutanen Edom suka yi a ranar da Urushalima ta fāɗi. Suka yi ihu suka ce, “A ragargaza ta, A ragargaza ta har tushenta!” |
| 8 |
| Ya Diyar Babilon, an ƙaddara ke zuwa hallaka, mai farin ciki ne wanda ya sāka miki saboda abin da kika yi mana, |
| 9 |
| shi da ya ƙwace jariranki ya fyaɗa su a kan duwatsu. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/137.mp3
150
137