Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Ya Ubangiji ka ji addu'ata, Ka kasa kunne ga roƙona! Kai adali ne mai aminci, Don haka ka amsa mini! |
| 2 |
| Ni bawanka, kada ka gabatar da ni a gaban shari'a, Gama ba wanda ba shi da laifi a gare ka. |
| 3 |
| Maƙiyina ya tsananta mini, Ya kore ni fata-fata. Ya sa ni a kurkuku mai duhu, Ina kama da waɗanda suka daɗe da mutuwa, |
| 4 |
| Don haka ina niyya in fid da zuciya, Ina cikin damuwa mai zurfi. |
| 5 |
| Na tuna kwanakin baya, Na tuna da dukan abin da ka yi, Na tuna da dukan ayyukanka. |
| 6 |
| Na ɗaga hannuwana sama, ina addu'a gare ka, Kamar busasshiyar ƙasa, raina yana jin ƙishinka. |
| 7 |
| Yanzu ka amsa mini, ya Ubangiji! Na fid da zuciya duka! Kada ka ɓuya mini, Don kada in zama cikin waɗanda suke gangarawa zuwa lahira. |
| 8 |
| A gare ka nake dogara, Da safe ka tuna mini da madawwamiyar ƙaunarka. Addu'ata ta hau zuwa gare ka, Ka nuna mini hanyar da zan bi. |
| 9 |
| Na tafi wurinka don ka kiyaye ni, ya Ubangiji, Ka cece ni daga maƙiyana. |
| 10 |
| Kai ne Allahna, Ka koya mini in aikata nufinka. Ka sa in sami alherin Ruhunka. Ka bi da ni a hanyar lafiya. |
| 11 |
| Ka cece ni, ya Ubangiji, kamar yadda ka alkawarta. Saboda alherinka ka tsamo ni daga wahalaina! |
| 12 |
| Saboda ƙaunar da kake yi mini, Ka kashe maƙiyana. Ka hallakar da dukan waɗanda suke zaluntata. Gama ni bawanka ne. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/psalms/143.mp3
150
143