Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ya Ubangiji, ka ji addu’ata, ka saurari kukata don neman jinƙai; cikin amincinka da adalcinka ka amsa mini. |
| 2 |
| Kada ka gabatar da bawanka a gaban shari’a, gama babu wani mai rai da yake adali a gabanka. |
| 3 |
| Abokin gāba yana fafarata, ya murƙushe ni har ƙasa; ya sa ina zama a cikin duhu kamar waɗanda suka mutu tun tuni. |
| 4 |
| Ta haka ƙarfina ya ƙare a cikina zuciyata ta damu ƙwarai. |
| 5 |
| Na tuna da kwanakin baya na yi tunani a kan dukan ayyukanka na kuma lura da abin da hannuwanka suka yi. |
| 6 |
| Na buɗe hannuwana gare ka; raina yana jin ƙishinka kamar busasshiyar ƙasa. |
| 7 |
| Ka amsa mini da sauri, ya Ubangiji; ƙarfina ya ƙare. Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni in ba haka ba zan zama kamar waɗanda suka gangara zuwa rami. |
| 8 |
| Bari safiya ta kawo mini maganar ƙaunarka marar ƙarewa, gama na sa zuciyata a gare ka. Ka nuna mini hanyar da zan bi, gama a gare ka na miƙa raina. |
| 9 |
| Ka cece ni daga abokan gābana, ya Ubangiji, gama na ɓoye kaina a gare ka. |
| 10 |
| Ka koya mini in yi nufinka, gama kai ne Allahna; bari nagarin Ruhunka yă bi da ni a ƙasar da ba gargaɗa. |
| 11 |
| Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka kiyaye raina; a cikin adalcinka, ka fid da ni daga wahala. |
| 12 |
| A cikin ƙaunarka marar ƙarewa, ka rufe bakunan abokan gābana; ka hallaka dukan maƙiyana, gama ni bawanka ne. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/143.mp3
150
143