|
| 1 |
|
| Zan yi shelar girmanka, ya Allahna, Sarkina, Zan yi maka godiya har abada abadin. |
|
| 2 |
|
| Kowace rana zan yi maka godiya, Zan yabe ka har abada abadin. |
|
| 3 |
|
| Ubangiji mai girma ne, dole ne a fifita yabonsa, Girmansa ya fi ƙarfin ganewa. |
|
| 4 |
|
| Za a yabi abin da ka aikata daga tsara zuwa tsara, Za su yi shelar manya manyan ayyukanka. |
|
| 5 |
|
| Mutane za su yi magana a kan darajarka da ɗaukakarka, Ni kuwa zan yi ta tunani a kan ayyukanka masu banmamaki. |
|
| 6 |
|
| Mutane za su yi magana a kan manya manyan ayyukanka, Ni kuwa zan yi shelar girmanka. |
|
| 7 |
|
| Za su ba da labarin girmanka duka, Su kuma raira waƙa a kan alherinka. |
|
| 8 |
|
| Ubangiji mai ƙauna ne, mai jinƙai, mai jinkirin fushi, Cike da madawwamiyar ƙauna. |
|
| 9 |
|
| Shi mai alheri ne ga kowa, Yana juyayin dukan abin da ya halitta. |
|
| 10 |
|
| Ya Ubangiji, talikanka duka za su yabe ka, Jama'arka kuma za su yi maka godiya! |
|
| 11 |
|
| Za su yi maganar darajar mulkinka, Su ba da labarin ikonka, |
|
| 12 |
|
| Domin haka dukan mutane za su san manyan ayyukanka, Da kuma darajar ɗaukakar mulkinka. |
|
| 13 |
|
| Mulkinka, madawwamin mulki ne, Sarki ne kai har abada. |
|
| 14 |
|
| Ubangiji, yakan taimaki dukan waɗanda yake shan wahala, Yakan ta da waɗanda aka wulakanta. |
|
| 15 |
|
| Dukan masu rai suna sa zuciya gare shi, Yana ba su abinci a lokacin da suke bukata, |
|
| 16 |
|
| Yana kuwa ba su isasshe, Yakan biya bukatarsu duka. |
|
| 17 |
|
| Ubangiji mai adalci ne a abin da yake yi duka, Mai jinƙai ne a ayyukansa duka. |
|
| 18 |
|
| Yana kusa da dukan waɗanda suke kira gare shi, Waɗanda suke kiransa da zuciya ɗaya. |
|
| 19 |
|
| Yakan biya bukatar dukan waɗanda suke tsoronsa, Yakan ji kukansu, ya cece su. |
|
| 20 |
|
| Yakan kiyaye dukan waɗanda suke ƙaunarsa, Amma zai hallaka mugaye duka. |
|
| 21 |
|
| A kullum zan yabi Ubangiji, Bari talikai duka su yabi sunansa mai tsarki har abada! |
|
|
|
|