Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Yabi Ubangiji. Yana da kyau a rera yabai ga Allahnmu, abu mai daɗi ne daidai ne kuma a yabe shi! |
| 2 |
| Ubangiji ya gina Urushalima; ya tattara kamammu na Isra’ilan da aka kai bauta. |
| 3 |
| Ya warkar da masu raunanar zuciya ya ɗaɗɗaura miyakunsu. |
| 4 |
| Ya lissafta yawan taurari ya kuma kira kowannensu da suna. |
| 5 |
| Shugabanmu mai girma ne mai iko duka; ganewarsa ba shi da iyaka. |
| 6 |
| Ubangiji yana kula da masu sauƙinkai yakan yar da mugaye a ƙasa. |
| 7 |
| Rera wa Ubangiji waƙar godiya; ku kada garaya ga Allahnmu. |
| 8 |
| Ya rufe sararin sama da gizagizai; yana tanada wa duniya ruwan sama yana kuma sa ciyawa tă yi girma a kan tuddai. |
| 9 |
| Yakan tanada wa shanu abinci da kuma saboda ’ya’yan hankaki sa’ad da suka yi kira. |
| 10 |
| Jin daɗinsa ba ya a ƙarfin doki, balle farin cikinsa yă kasance a ƙafafun mutum; |
| 11 |
| Ubangiji yakan yi farin ciki a waɗanda suke tsoronsa, waɗanda suke sa zuciya a ƙaunarsa marar ƙarewa. |
| 12 |
| Ki ɗaukaka Ubangiji, ya Urushalima; ki yabi Allahnki, ya Sihiyona. |
| 13 |
| Gama yana ƙarfafa ƙyamaren ƙofofinki yana kuma albarkace mutanenki a cikinki. |
| 14 |
| Yana ba da salama ga iyakokinki yana kuma ƙosar da ke da alkama mafi kyau. |
| 15 |
| Yana ba da umarninsa ga duniya; maganarsa tana tafiya da sauri. |
| 16 |
| Yana shimfiɗa ƙanƙara kamar ulu yă kuma watsar da hazo kamar toka. |
| 17 |
| Yana zuba ƙanƙara kamar ƙananan duwatsu. Wa zai iya jure wa sanyin da ya aiko? |
| 18 |
| Yakan aiki maganarsa ta kuwa narkar da su; yakan tā da iskarsa, ruwaye kuwa su gudu. |
| 19 |
| Ya bayyana maganarsa ga Yaƙub, dokokinsa da ƙa’idodinsa ga Isra’ila. |
| 20 |
| Bai yi wannan ga wata al’umma ba; ba su san dokokinsa ba. Yabi Ubangiji. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/147.mp3
150
147