Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Yabi Ubangiji. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, yabonsa a cikin taron tsarkaka. |
| 2 |
| Bari Isra’ila su yi farin ciki da Mahaliccinsu; bari mutanen Sihiyona su yi murna da Sarkinsu. |
| 3 |
| Bari su yabi sunansa tare da rawa suna kuma yin kiɗi gare shi da ganga da garaya. |
| 4 |
| Gama Ubangiji yana jin daɗin mutanensa; yakan darjanta masu sauƙinkai da ceto. |
| 5 |
| Bari tsarkaka su yi farin ciki a wannan bangirma su kuma rera don farin ciki a kan gadajensu. |
| 6 |
| Bari yabon Allah yă kasance a bakunansu takobi mai kaifi kuma a hannuwansu, |
| 7 |
| don su ɗau fansa a kan al’ummai da kuma hukunci a kan mutane, |
| 8 |
| don su ɗaura sarakuna da sarƙoƙi, manyan garinsu da sarƙoƙin ƙarfe, |
| 9 |
| don su yi hukuncin da aka rubuta a kansu. Wannan ne ɗaukakar dukan tsarkakansa. Yabi Ubangiji. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/149.mp3
150
149