Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Wane ne zai iya zama cikin Haikalinka? Wa zai iya tsayawa a Sihiyona, wato tudunka tsattsarka? |
| 2 |
| Sai dai mutumin da yake biyayya ga Allah da kowane abu, Yana kuwa aikata abin da yake daidai, Wanda yake faɗar gaskiya da zuciya ɗaya, |
| 3 |
| Wanda kuma ba ya ɓāta sunan waɗansu. Ba ya zargin abokansa, Ba ya kuwa baza jita-jita a kan maƙwabtansa. |
| 4 |
| Yakan raina waɗanda Allah ya ƙi su, Amma yana girmama waɗanda suke yi wa Ubangiji biyayya, Kullum yana cika alkawaran da ya yi ko ta halin ƙaƙa, |
| 5 |
| Yana ba da rance ba ruwa, Ba ya karɓar hanci don ya yi shaidar zur a kan marar laifi. Wanda ya aikata waɗannan abubuwa ba zai taɓa fāɗuwa ba. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/psalms/015.mp3
150
15