Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Ya Allah, ka kiyaye ni, gama na zo gare ka neman mafaka. |
| 2 |
| Na ce wa Ubangiji, “Kai ne Ubangijina, Dukan kyawawan abubuwan da nake da su Daga gare ka suke.” |
| 3 |
| Dubi irin martabar da amintattun jama'ar Ubangiji suke da ita! Ba abin da raina ya fi so, Sai in zauna tare da su. |
| 4 |
| Waɗanda suke hanzari zuwa ga gumaka, Za su jawo wa kansu wahala. Ba zan yi tarayya da su da hadayarsu ba. Ba zan yi sujada ga gumakansu ba. |
| 5 |
| Kai ne kaɗai, nake da shi, ya Ubangiji, Kai ne kake biyan dukan bukatata, Raina yana hannunka. |
| 6 |
| Kyautanka zuwa gare ni da bansha'awa suke, Kyawawa ne kuwa ƙwarai! |
| 7 |
| Na yabi Ubangiji saboda yana bi da ni, Da dare kuma lamirina yana yi mini fadaka. |
| 8 |
| A kullum ina jin Ubangiji yana tare da ni, Yana nan kusa, ba abin da zai girgiza ni. |
| 9 |
| Don haka cike nake da murna da farin ciki, Kullum kuwa ina jin kome lafiya yake, |
| 10 |
| Saboda ba za ka yarda in shiga lahira ba, Ba za ka bar wanda kake ƙauna a zurfafa daga ƙarƙas ba. |
| 11 |
| Za ka nuna mini hanyar rai, Kasancewarka takan sa in cika da farin ciki, Taimakonka kuwa yana kawo jin daɗi har abada. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/psalms/016.mp3
150
16