Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ka kiyaye ni, ya Allah, gama a cikinka nake samun mafaka. |
| 2 |
| Na ce wa Ubangiji, “Kai ne shugabana; in ba tare da kai ba, ba ni da wani abu mai kyau.” |
| 3 |
| Game da tsarkakan da suke cikin ƙasar kuwa, su ne masu ɗaukakar da dukan farin cikina ya dangana. |
| 4 |
| Baƙin ciki zai ƙaru wa waɗanda suke bin waɗansu alloli. Ba zan zuba musu hadayarsu ta jini ba ko in ambaci sunayensu da bakina. |
| 5 |
| Ubangiji, ka ba ni rabona da kwaf ɗin na; ka kiyaye rabona, |
| 6 |
| Iyakoki sun fāɗo mini a wurare masu daɗi; tabbatacce ina da gādo mai bansha’awa. |
| 7 |
| Zan yabi Ubangiji, wanda yake ba ni shawara; ko da dare ma zuciyata kan koya mini. |
| 8 |
| Kullum nakan sa Ubangiji a gabana. Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba. |
| 9 |
| Saboda haka zuciyata tana murna harshena kuma yana farin ciki; jikina kuma zai zauna lafiya, |
| 10 |
| domin ba za ka yashe ni a kabari ba, ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba. |
| 11 |
| Ka sanar da ni hanyar rai; za ka cika ni da farin ciki a gabanka, da madawwamin jin daɗi a hannun damarka. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/016.mp3
150
16