Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ina ƙaunarka, ya Ubangiji, ƙarfina. |
| 2 |
| Ubangiji shi ne dutsena, kagarata da kuma mai cetona; Allahna shi ne dutsena, a gare shi nake neman mafaka. Shi ne garkuwata da ƙahon cetona, mafakata. |
| 3 |
| Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo, na kuwa kuɓuta daga abokan gābana. |
| 4 |
| Igiyoyin mutuwa sun shaƙe ni; rigyawan hallaka sun sha kaina. |
| 5 |
| Igiyoyin mutuwa sun nannaɗe kewaye da ni; tarkon mutuwa ya yi mini arangama. |
| 6 |
| Cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji; Na yi kuka ga Allahna don taimako. A Haikalinsa ya ji muryata, Kukana na neman taimako ya kai kunnensa. |
| 7 |
| Ƙasa ta yi rawa ta kuma girgiza, tussan duwatsu sun girgiza; sun yi rawa domin ya yi fushi. |
| 8 |
| Hayaƙi ya tashi daga kafan hancinsa; wuta mai ci daga bakinsa, garwashi wuta mai ci daga bakinsa. |
| 9 |
| Ya buɗe sammai ya sauko; baƙaƙen gizagizai suna a ƙarƙashin ƙafafunsa. |
| 10 |
| Ya hau kerubobi ya kuma yi firiya; ya yi shawagi a fikafikan iska. |
| 11 |
| Ya mai da duhu abin rufuwarsa, rumfa kewaye da shi, baƙaƙen gizagizan ruwan sama na sarari, |
| 12 |
| daga cikin hasken kasancewarsa gizagizai suka yi gaba, da ƙanƙara da kuma walƙiya. |
| 13 |
| Ubangiji ya yi tsawa daga sama; muryar Mafi Ɗaukaka ya yi kāra. |
| 14 |
| Ya harba kibiyoyinsa ya kuma watsar da abokan gāba, walƙiya mai girma ya fafare su. |
| 15 |
| Kwarin teku sun bayyana tussan duniya sun bayyana a fili sa’ad da ka tsawata, ya Ubangiji, sa’ad da ka numfasa daga hancinka. |
| 16 |
| Ya miƙa hannunsa daga sama ya kama ni; ya ja ni daga zurfin ruwaye. |
| 17 |
| Ya cece ni daga abokin gābana mai ƙarfi, daga abokan gābana, waɗanda suka fi ƙarfina. |
| 18 |
| Sun yi arangama da ni a ranar masifa, amma Ubangiji ya zama mai taimakona. |
| 19 |
| Ya fitar da ni zuwa wuri mai sarari; ya kuɓutar da ni, gama yana jin daɗina. |
| 20 |
| Ubangiji ya yi haka da ni bisa ga adalcina; bisa ga tsabtar hannuwana ya ba ni lada. |
| 21 |
| Gama na kiyaye hanyoyin Ubangiji; ban yi mugunta ta wurin juyewa daga Allahna ba. |
| 22 |
| Dukan dokokinsa suna a gābana; ban juye daga ƙa’idodinsa ba. |
| 23 |
| Na kasance marar laifi a gabansa na kuma kiyaye kaina daga zunubi. |
| 24 |
| Ubangiji ya ba ni lada bisa ga adalcina, bisa ga tsabtan hannuwana a gabansa. |
| 25 |
| Ga mai aminci ka nuna kanka mai aminci, ga marar laifi ka nuna kanka marar laifi, |
| 26 |
| ga mai tsabta ka nuna kanka mai tsabta, amma ga karkatacce, ka nuna kanka mai wayo. |
| 27 |
| Kakan cece mai sauƙinkai amma kakan ƙasƙantar da masu girman kai. |
| 28 |
| Kai Ya Ubangiji, ka sa fitilata ta yi ta ci; Allahna ya mai da duhu ya zama haske. |
| 29 |
| Da taimakonka zan iya fāɗa wa runduna; tare da Allahna zan iya rinjayi katanga. |
| 30 |
| Game da Allah kuwa, hanyarsa cikakkiya ce; maganar Ubangiji marar kuskure ne. Shi garkuwa ne ga dukan waɗanda suke neman mafaka a gare shi. |
| 31 |
| Gama wane ne Allah in ba Ubangiji ba? Wane ne kuwa Dutse in ba Allahnmu ba? |
| 32 |
| Allah ne ya ƙarfafa ni da ƙarfi ya kuma sa hanyarta ta zama cikakkiya. |
| 33 |
| Ya sa ƙafafuna kamar ƙafafun barewa; ya sa na iya tsaya a kan ƙwanƙoli. |
| 34 |
| Ya horar da hannuwana don yaƙi; hannuwana za su iya tanƙware bakan tagulla. |
| 35 |
| Ka ba ni garkuwar nasara, kuma hannunka na dama yana riƙe ni; ya sunkuya don ka mai da ni mai girma. |
| 36 |
| Ka fadada hanyar da yake a ƙarƙashina, don kada ɗiɗɗigena yă juya. |
| 37 |
| Na bi abokan gābana na kuma cim musu; ban juya ba sai da na hallaka su. |
| 38 |
| Na ragargaza su har ba za su iya tashi ba; sun fāɗi a ƙarƙashin ƙafafuna. |
| 39 |
| Ka ƙarfafa ni da ƙarfi saboda yaƙi; ka sa abokan gābana suka rusuna mini. |
| 40 |
| Ka sa abokan gābana suka juya suka gudu, na kuma hallaka abokan gābana. |
| 41 |
| Sun nemi taimako, amma ba su sami wanda zai cece su ba, ga Ubangiji, amma bai amsa ba. |
| 42 |
| Na murƙushe su kamar ƙura mai laushi da iska ke kwashewa; na zubar da su kamar laka a tituna. |
| 43 |
| Ka cece ni daga harin mutane; ka mai da ni kan al’ummai. Mutanen da ban sani ba sun zama bayina, |
| 44 |
| da zarar sun ji ni, sukan yi mini biyayya; baƙi suna rusuna a gabana. |
| 45 |
| Duk sukan karai; suna zuwa da rawan jiki daga mafakansu. |
| 46 |
| Ubangiji mai rai ne! Yabo ya tabbata ga Dutsena! Girma ya tabbata ga Allah Mai cetona! |
| 47 |
| Shi ne Allah mai sāka mini, wanda yake sa al’ummai a ƙarƙashina, |
| 48 |
| wanda yakan cece ni daga abokan gābana. Ana girmama ka bisa abokan gābana; daga masu tā-da-na-zaune-tsaye ka kuɓutar da ni. |
| 49 |
| Saboda haka zan yabe ka a cikin al’ummai, ya Ubangiji; zan rera yabai ga sunanka. |
| 50 |
| Yakan ba sarkinsa nasarori; yakan nuna alheri marar ƙarewa ga shafaffensa, ga Dawuda da zuriyarsa har abada. |
|
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/018.mp3
150
18