Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Me ya sa ƙasashe suke haɗa baki mutane kuma suke ƙulla shawarwarin banza? |
| 2 |
| Sarakunan duniya sun ɗauki matsayi masu mulki sun taru gaba ɗaya suna gāba da Ubangiji da kuma Shafaffensa. |
| 3 |
| Suna cewa, “Bari mu tsittsinke sarƙoƙinsu, mu kuma ’yantar da kamammu daga kangin bautar Allah.” |
| 4 |
| Mai zama a kursiyi a sama yana dariya; Ubangiji yana musu ba’a. |
| 5 |
| Sa’an nan ya tsawata musu cikin fushinsa ya kuma razanar da su cikin hasalarsa, yana cewa, |
| 6 |
| “Na kafa Sarkina a kan kursiyi a kan Sihiyona, dutsena mai tsarki.” |
| 7 |
| Sarki ya yi shelar umarnin Ubangiji. Ubangiji ya ce mini, “Kai Ɗana ne; yau na zama Mahaifinka. |
| 8 |
| Ka tambaye ni zan kuwa sa al’ummai su zama gādonka, iyakokin duniya su zama mallakarka. |
| 9 |
| Za ka yi mulkinsu da sandan ƙarfe; za ka farfashe su kucu-kucu kamar tukunyar laka.” |
| 10 |
| Saboda haka, ku sarakuna, ku yi wayo; ku shiga hankalinku, ku masu mulkin duniya. |
| 11 |
| Ku bauta wa Ubangiji da tsoro ku kuma yi farin ciki kuna rawar jiki. |
| 12 |
| Ku sumbaci Ɗan, don kada yă yi fushi ku hallaka a abubuwan da kuke yi, gama fushinsa zai iya kuna farat ɗaya. Masu farin ciki ne dukan waɗanda suke neman mafaka daga gare shi. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/002.mp3
150
2