Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba, |
| 2 |
| Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa, yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya, |
| 3 |
| yakan maido da raina. Yakan bi da ni a hanyoyin adalci saboda sunansa. |
| 4 |
| Ko da na yi tafiya ta kwari na inuwar mutuwa, ba zan ji tsoron mugu ba, gama kana tare da ni; bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya, za su yi mini ta’aziyya. |
| 5 |
| Ka shirya mini tebur a gaban abokan gābana. Ka shafe kaina da mai; kwaf nawa ya cika har yana zuba. |
| 6 |
| Tabbatacce alheri da ƙauna za su bi dukan kwanakin raina, zan kuwa zauna a gidan Ubangiji har abada. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/023.mp3
150
23