Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Duniya ta Ubangiji ce da kome da yake cikinta, duniya, da dukan waɗanda suke zama a cikinta; |
| 2 |
| gama ya gina ta a kan tekuna ya kafa ta a kan ruwaye. |
| 3 |
| Wa zai iya hawan tudun Ubangiji? Wa zai iya tsaya a wurinsa mai tsarki? |
| 4 |
| Sai wanda yake da hannu mai tsabta da kuma tsabtar zuciya, wanda ba ya ba da ransa ga bautar gunki ko ya rantse bisa abin da yake ƙarya. |
| 5 |
| Zai sami albarka daga Ubangiji da fiffitawa daga Allah Mai cetonsa. |
| 6 |
| Irin tsaran waɗanda suke nemansa ke nan, waɗanda suke neman fuskarka, ya Allah na Yaƙub. |
| 7 |
| Ku ɗaga kawunanku, ya ku ƙofofi; ku ɗagu, ku daɗaɗɗun ƙofofi, don Sarkin ɗaukaka yă shiga. |
| 8 |
| Wane ne wannan Sarkin ɗaukaka? Ubangiji ne mai ƙarfi mai iko, Ubangiji mai girma a yaƙi. |
| 9 |
| Ku ɗaga kawunanku, ya ku ƙofofi; ku ɗagu, ku daɗaɗɗun ƙofofi, don Sarkin ɗaukaka yă shiga. |
| 10 |
| Wane ne shi, wannan Sarkin ɗaukaka? Ubangiji Maɗaukaki, shi ne Sarkin ɗaukaka. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/024.mp3
150
24