Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| A gare ka nake yin addu'a, ya Ubangiji, |
| 2 |
| A gare ka nake dogara, ya Allah. Ka cece ni daga shan kunyar fāɗuwa, Kada ka bar magabtana su yi mini duban wulakanci! |
| 3 |
| Waɗanda suke dogara gare ka, Ba za su kasa yin nasara ba, Sai dai waɗanda suke gaggawa su yi maka tayarwa. |
| 4 |
| Ka koya mini al'amuranka, ya Ubangiji, Ka sa su zama sanannu a gare ni. |
| 5 |
| Ka koya mini in yi zamana bisa ga gaskiyarka, Gama kai Mai Cetona ne. Dukan yini ina dogara a gare ka. |
| 6 |
| Ya Ubangiji, ka tuna da alherinka da madawwamiyar ƙaunarka, Waɗanda ka nuna tun a dā. |
| 7 |
| Ka gafarta zunubaina da kurakuraina masu yawa na ƙuruciyata. Saboda madawwamiyar ƙaunarka da alherinka, Ka tuna da ni, ya Ubangiji! |
| 8 |
| Ubangiji mai adalci ne, mai alheri, Yana koya wa masu zunubi tafarkin da za su bi. |
| 9 |
| Yana bi da masu tawali'u a tafarkin da suke daidai, Yana koya musu nufinsa. |
| 10 |
| Da ƙauna da aminci yana bi da dukan waɗanda suke biyayya da alkawarinsa da umarnansa. |
| 11 |
| Ka cika alkawarinka, ya Ubangiji, ka gafarta zunubaina, gama suna da yawa. |
| 12 |
| Waɗanda suke biyayya da Ubangiji Za su koyi hanyar da za su bi daga gare shi. |
| 13 |
| Kullayaumi za su arzuta, 'Ya'yansu kuma za su zauna lafiya a ƙasar. |
| 14 |
| Ubangiji yakan amince da waɗanda suke biyayya da shi, Yakan koya musu alkawarinsa. |
| 15 |
| A koyaushe ga Ubangiji nake neman taimako, Yakan kuɓutar da ni daga hatsari. |
| 16 |
| Ka juyo wajena, ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai, Gama ina zaman kaɗaici da rashin ƙarfi. |
| 17 |
| Damuwar zuciyata ta yi yawa, Ka raba ni da dukan damuwa, Ka cece ni daga dukan wahalata. |
| 18 |
| Ka kula da wahalata da azabata, Ka gafarta dukan zunubaina. |
| 19 |
| Ka duba yawan magabtan da nake da su, Dubi irin ƙiyayyar da suke yi mini! |
| 20 |
| Ka yi mini kāriya, ka cece ni, Gama na zo wurinka neman kāriya. |
| 21 |
| Ka sa nagartata da amincina su kiyaye ni, Gama na dogara gare ka. |
| 22 |
| Ka fanshi jama'arka daga dukan wahalarsu, ya Allah! |
|
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/psalms/025.mp3
150
25