Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Ka hurta rashin laifina, ya Ubangiji, Gama na yi abin da suke daidai, Na dogara gare ka gaba ɗaya. |
| 2 |
| Ka jarraba ni ka auna ni, ya Ubangiji, Ka gwada muradina da tunanina. |
| 3 |
| Madawwamiyar ƙaunarka tana bi da ni, Amincinka yake yi mini jagora kullayaumin. |
| 4 |
| Ba na tarayya da mutanen banza, Ba abin da ya gama ni da masu riya. |
| 5 |
| Ina ƙin tarayya da masu mugunta, Nakan kauce wa mugaye. |
| 6 |
| Ya Ubangiji, na wanke hannuwana Don in nuna ba ni da laifi, Da ibada nakan taka, ina kewaya bagadenka. |
| 7 |
| Na raira waƙar godiya, Na faɗi dukan ayyukanka masu banmamaki. |
| 8 |
| Ya Ubangiji, ina ƙaunar Haikali inda zatinka yake, Inda ɗaukakarka yake zaune. |
| 9 |
| Kada ka hallaka ni tare da masu zunubi, Ka cece ni daga ƙaddarar masu kisankai, |
| 10 |
| Mutanen da suke aikata mugunta a dukan lokaci, A koyaushe suna shirye don su ba da rashawa. |
| 11 |
| Amma ni, ina yin abin da yake daidai, Ka yi mini jinƙai ka fanshe ni! |
| 12 |
| Na kuɓuta daga dukan hatsarori, A taron sujada na yabi Ubangiji! |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/psalms/026.mp3
150
26