Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| A gare ka nake kira, ya Ubangiji Dutsena; kada ka yi mini kunnen ƙashi. Gama in ka yi shiru, zan zama kamar waɗanda suka gangara rami. |
| 2 |
| Ka ji kukata ta neman jinƙai yayinda nake kira ka don neman taimako, yayinda nake daga hannuwana wajen Wurinka Mafi Tsarki. |
| 3 |
| Kada ka ja ni tare da mugaye, tare da masu yin mugunta, masu magana kamar ta alheri ce da maƙwabtansu amma suna riƙe da su a zukatansu. |
| 4 |
| Ka sāka musu da ayyukansu da kuma don mugun aikinsu; ka sāka musu saboda abin da hannuwansu suka yi ka kuma mayar musu abin da ya dace da su. |
| 5 |
| Da yake ba su kula da ayyukan Ubangiji da abin da hannuwansa suka yi ba, zai rushe su ba kuwa zai ƙara gina su ba. |
| 6 |
| Yabo ya tabbata ga Ubangiji, gama ya ji kukata na neman jinƙai. |
| 7 |
| Ubangiji shi ne ƙarfina da garkuwata; zuciyata ta amince da shi, kuma na sami taimako. Zuciyata ta yi tsalle don farin ciki zan kuwa yi godiya gare shi cikin waƙa. |
| 8 |
| Ubangiji shi ne ƙarfin mutanensa, kagarar ceto domin shafaffensa. |
| 9 |
| Ka cece mutanenka ka kuma albarkace gādonka; ka zama mai kiwonsu ka kuma riƙe su har abada. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/028.mp3
150
28