Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ya Ubangiji, abokan gābana nawa ne! Su nawa suke gāba da ni! |
| 2 |
| Da yawa suna magana a kaina suna cewa, “Allah ba zai cece shi ba.” |
| 3 |
| Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji; ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina. |
| 4 |
| Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi, ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. |
| 5 |
| Na kwanta na yi barci; na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni. |
| 6 |
| Ba zan ji tsoro ko dubu goma suka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba. |
| 7 |
| Ka tashi Ya Ubangiji! Ka cece ni, ya Allahna! Ka bugi dukan abokan gābana a muƙamuƙi; ka kakkarya haƙoran mugaye. |
| 8 |
| Daga wurin Ubangiji ne ceto kan zo. Bari albarkanka yă kasance a kan mutanenka. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/003.mp3
150
3