Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Ina yabonka, ya Ubangiji saboda ka cece ni, Ka kuwa hana magabtana su haɗiye ni. |
| 2 |
| Na roƙi taimako a gare ka, ya Ubangiji Allahna, Ka kuwa warƙar da ni. |
| 3 |
| Ka dawo da ni daga lahira. Na gangara tare da waɗanda suke gangarawa cikin zurfafa a ƙasa, Amma ka ceci raina. |
| 4 |
| Ku raira yabo ga Ubangiji, Ku amintattun jama'arsa! Ku tuna da abin da Mai Tsarki ya aikata, Ku yi masa godiya! |
| 5 |
| Fushinsa ba ya daɗewa, Alherinsa kuwa har matuƙa ne. Mai yiwuwa ne yă zama ana kuka da dare, Amma a yi murna da safe. |
| 6 |
| Ina zaune jalisan, na ce wa kaina, “Faufau ba za a taɓa cin nasara a kaina ba.” |
| 7 |
| Kana yi mini alheri, ya Ubangiji, Ka kiyaye ni kamar a kagarar dutse. Amma sa'ad da ka ɓoye mini fuskarka, Sai in cika da tsoro. |
| 8 |
| Ina kira gare ka, ya Ubangiji, Ina roƙon taimakonka. |
| 9 |
| Wane amfani za a samu daga mutuwata? Ina ribar da za a samu daga zuwana kabari? Ko matattu suna iya yabonka? Za su iya shelar madawwamin alherinka? |
| 10 |
| Ka ji ni, ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai! Ka taimake ni, ya Ubangiji! |
| 11 |
| Ka mai da baƙin cikina Ya zama rawar farin ciki, Ka tuɓe mini tufafin makoki, Ka sa mini na farin ciki. |
| 12 |
| Don haka ba zan yi shiru ba, Zan raira maka yabo, Ya Ubangiji, kai ne Allahna, Zan gode maka har abada. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/psalms/030.mp3
150
30