Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Zan girmama ka Ya Ubangiji, gama ka tsamo ni daga zurfafa ba ka bar abokan gābana sun yi farin ciki a kaina ba. |
| 2 |
| Ya Ubangiji Allahna, na yi kira gare ka don taimako ka kuwa warkar da ni. |
| 3 |
| Ya Ubangiji, ka dawo da ni daga kabari; ka kiyaye ni daga gangarawa zuwa cikin rami. |
| 4 |
| Ku rera ga Ubangiji, ku tsarkakansa; ku yabi sunansa mai tsarki. |
| 5 |
| Gama fushinsa na ɗan lokaci ne amma alherinsa har matuƙa ne; mai yiwuwa a yi kuka da dare amma farin ciki kan zo da safe. |
| 6 |
| Sa’ad da nake lafiya, na ce, “Ba zan jijjigu ba.” |
| 7 |
| Ya Ubangiji, sa’ad da ka yi mini alheri, ka sa katangar dutsena ya tsaya daram; amma sa’ad da ka ɓoye fuskarka, sai in cika da tsoro. |
| 8 |
| A gare ka, ya Ubangiji, na yi kira; a gare ka Ubangiji na yi kukan neman jinƙai. |
| 9 |
| “Wace riba ce a hallakata, a kuma gangarawa ta zuwa cikin rami? Ƙura za tă yabe ka ne? Za tă iya yin shelar amincinka? |
| 10 |
| Ka ji, ya Ubangiji, ka kuwa yi mini jinƙai; Ya Ubangiji, ka zama taimakona.” |
| 11 |
| Ka mai da kukata ta zama rawa; ka tuɓe rigar makokina ka sa mini na farin ciki, |
| 12 |
| don zuciyata za tă iya rera gare ka ba kuwa za tă yi shiru ba. Ya Ubangiji Allahna, zan yi maka godiya har abada. |
|
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/030.mp3
150
30