|
| 1 |
|
| Dukanku adalai ku yi murna, A kan abin da Ubangiji ya yi, Ku yabe shi, ku da kuke masa biyayya! |
|
| 2 |
|
| Ku kaɗa garaya, kuna yi wa Ubangiji godiya. Ku raira masa waƙa, da kayan kaɗe-kaɗe masu tsarkiya. |
|
| 3 |
|
| Ku raira masa sabuwar waƙa, Ku kaɗa garaya da gwaninta, Ku kuma raira waƙa da ƙarfi! |
|
| 4 |
|
| Kalmomin Ubangiji gaskiya ne, Ayyukansa duka kuwa abin dogara ne. |
|
| 5 |
|
| Ubangiji yana ƙaunar abin da yake na adalci da gaskiya, Madawwamiyar ƙaunarsa ta cika duniya. |
|
| 6 |
|
| Ubangiji ya halicci duniya da umarninsa, Rana, da wata, da taurari kuma bisa ga maganarsa. |
|
| 7 |
|
| Ya tattara tekuna wuri ɗaya. Ya rurrufe zurfafan teku a ɗakunan ajiya. |
|
| 8 |
|
| Bari duk duniya ta ji tsoron Ubangiji! Ku ji tsoronsa ku mutanen duniya! |
|
| 9 |
|
| Da magana ya halicci duniya, Ta wurin umarninsa kowane abu ya bayyana. |
|
| 10 |
|
| Ubangiji yakan sassoke manufofin sauran al'umma, Yakan hana su aikata shirye-shiryensu. |
|
| 11 |
|
| Amma shirye-shiryensa sukan tabbata har abada. Nufe-nufensa kuma dawwamammu ne har abada. |
|
| 12 |
|
| Mai farin ciki ce al'ummar da Ubangiji yake Allahnta, Masu farin ciki ne jama'ar da Ubangiji ya zaɓo wa kansa! |
|
| 13 |
|
| Daga Sama Ubangiji ya dubo dukan 'yan adam. |
|
| 14 |
|
| Daga inda yake mulki, yakan dubo dukan mazaunan duniya. |
|
| 15 |
|
| Shi ya siffata tunaninsu, yana sane da dukan abin da suke yi. |
|
| 16 |
|
| Ba saboda ƙarfin mayaƙa sarki yakan ci nasara ba, Mayaƙi ba yakan yi rinjaye saboda ƙarfinsa ba. |
|
| 17 |
|
| Dawakan yaƙi ba su da amfani don cin nasara, Ƙarfin nan nasu ba zai iya ceto ba. |
|
| 18 |
|
| Ubangiji yana kiyaye masu tsoronsa, Waɗanda suke dogara ga madawwamiyar ƙaunarsa. |
|
| 19 |
|
| Yakan cece su daga mutuwa, Yakan rayar da su a lokacin yunwa. |
|
| 20 |
|
| Ga Ubangiji muke sa zuciya, Shi mai taimakonmu ne, mai kiyaye mu. |
|
| 21 |
|
| Saboda da shi muke murna, Muna dogara ga sunansa mai tsarki. |
|
| 22 |
|
| Ka sa madawwamiyar ƙaunarka ta kasance tare da mu, ya Ubangiji, Da yake a gare ka muke sa zuciya. |
|
|
|
|