|
| 1 |
|
| Ku rera da farin ciki ga Ubangiji ku adalai; daidai ne masu gaskiya su yabe shi. |
|
| 2 |
|
| Ku yabi Ubangiji da garaya; ku yi kiɗi gare shi da molo mai tsirkiya goma. |
|
| 3 |
|
| Ku rera masa sabuwar waƙa; ku yi kiɗi da gwaninta, ku kuma yi sowa don farin ciki. |
|
| 4 |
|
| Gama maganar Ubangiji daidai ne da kuma gaskiya; yana da aminci cikin kome da yake yi. |
|
| 5 |
|
| Ubangiji yana ƙaunar adalci duniya ta cika da ƙaunarsa marar ƙarewa. |
|
| 6 |
|
| Ta wurin maganar Ubangiji aka yi sammai, rundunar taurarinsu kuwa da numfashin bakinsa. |
|
| 7 |
|
| Ya tattara ruwan teku cikin tuluna; ya sa zurfafa cikin gidajen ajiya. |
|
| 8 |
|
| Bari dukan duniya ta ji tsoron Ubangiji; bari dukan mutanen duniya su girmama shi. |
|
| 9 |
|
| Gama ya yi magana, abu ya kuwa kasance; ya umarta, ya kuwa tsaya daram. |
|
| 10 |
|
| Ubangiji yakan soke shirye-shiryen al’ummai; yakan wofintar da manufofin mutane. |
|
| 11 |
|
| Amma shirye-shiryen Ubangiji kan tsaya daram har abada, manufofin zuciyarsa kuwa har dukan zamanai. |
|
| 12 |
|
| Mai farin ciki ce al’ummar da Allah ne Ubangijinta, mutanen da ya zaɓa don gādonsa. |
|
| 13 |
|
| Daga sama Ubangiji ya duba ya kuwa ga dukan ’yan adam; |
|
| 14 |
|
| daga mazauninsa yana lura da dukan waɗanda suke zama a duniya, |
|
| 15 |
|
| shi da ya yi zukatan duka, wanda yake kula da kome da suke yi. |
|
| 16 |
|
| Babu sarkin da ake ceto ta wurin yawan mayaƙansa; ba jarumin da kan kuɓuta ta wurin yawan ƙarfinsa. |
|
| 17 |
|
| Dogara a kan doki don ceto banza ne; duk da yawan ƙarfinsa ba ya ceto. |
|
| 18 |
|
| Amma idanun Ubangiji suna a kan wanda yake tsoronsa, a kan waɗanda suke sa zuciya cikin ƙaunarsa marar ƙarewa, |
|
| 19 |
|
| don yă cece su daga mutuwa ya bar su da rai a lokacin yunwa. |
|
| 20 |
|
| Muna jiran Ubangiji da bege; shi ne taimakonmu da garkuwarmu. |
|
| 21 |
|
| A cikinsa zukatanmu na farin ciki, gama mun dogara cikin sunansa mai tsarki. |
|
| 22 |
|
| Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zauna a kanmu, ya Ubangiji, ko ma da muke sa begenmu a gare ka. |
|
|
|
|