|
| 1 |
|
| Zan yi godiya ga Ubangiji kullayaumin, Faufau ba zan taɓa fasa yabonsa ba. |
|
| 2 |
|
| Zan yabe shi saboda abin da ya yi, Da ma dukan waɗanda suke da tawali'u su kasa kunne, su yi murna! |
|
| 3 |
|
| Ku yi shelar girman Ubangiji tare da ni, Mu yabi sunansa tare! |
|
| 4 |
|
| Na yi addu'a ga Ubangiji, ya kuwa amsa mini, Ya kuɓutar da ni daga dukan tsorona. |
|
| 5 |
|
| Waɗanda ake zalunta suka dube shi suka yi murna, Ba za su ƙara ɓacin rai ba. |
|
| 6 |
|
| Marasa galihu suka yi kira gare shi, ya kuwa amsa. Ya cece su daga dukan wahalarsu. |
|
| 7 |
|
| Mala'ikansa yana tsaron waɗanda suke tsoron Ubangiji, Ya cece su daga hatsari. |
|
| 8 |
|
| Ku gane da kanku yadda Ubangiji yake da alheri! Mai farin ciki ne mutumin da ya sami kwanciyar rai a wurinsa! |
|
| 9 |
|
| Ku yi tsoron Ubangiji ku jama'arsa duka, Masu tsoronsa suna da dukan abin da suke bukata. |
|
| 10 |
|
| Har zakoki sukan rasa abinci su ji yunwa, Amma masu biyayya ga Ubangiji, Ba abu mai kyau da sukan rasa. |
|
| 11 |
|
| Ku zo, ku abokaina, ku kasa kunne gare ni, Zan koya muku ku ji tsoron Ubangiji. |
|
| 12 |
|
| Kuna so ku ji daɗin rai? Kuna son tsawon rai da farin ciki? |
|
| 13 |
|
| To, ku yi nisa da mugun baki, Da faɗar ƙarairayi. |
|
| 14 |
|
| Ku rabu da mugunta, ku aikata alheri, Ku yi marmarin salama, ku yi ƙoƙarin samunta. |
|
| 15 |
|
| Ubangiji yana lura da adalai, Yana kasa kunne ga koke-kokensu, |
|
| 16 |
|
| Amma yana ƙin masu aikata mugunta, Saboda haka har mutanensu sukan manta da su. |
|
| 17 |
|
| Adalai sukan yi kira ga Ubangiji, yakan kuwa kasa kunne, Yakan cece su daga dukan wahalarsu. |
|
| 18 |
|
| Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai, Yakan ceci waɗanda suka fid da zuciya. |
|
| 19 |
|
| Mutumin kirki yakan sha wahala da yawa, Amma Ubangiji yakan cece shi daga cikinsu duka. |
|
| 20 |
|
| Ubangiji yakan kiyaye shi sosai, Ba ko ɗaya daga cikin ƙasusuwansa da zai karye ba. |
|
| 21 |
|
| Mugunta za ta kashe mugu, Waɗanda suke ƙin adalai za a hukunta su. |
|
| 22 |
|
| Ubangiji zai fanshi bayinsa, Waɗanda suka tafi wurinsa neman mafaka Za a bar su da rai. |
|
|
|
|