|
| 1 |
|
| Zan gode wa Ubangiji kullayaumi; yabonsa kullum za su kasance a leɓunana. |
|
| 2 |
|
| Raina zai yi fariya a cikin Ubangiji; bari waɗanda suke wahala su ji su kuma yi farin ciki. |
|
| 3 |
|
| Ku ɗaukaka Ubangiji tare da ni; bari mu ɗaukaka sunansa tare. |
|
| 4 |
|
| Na nemi Ubangiji, ya kuwa amsa mini; ya cece ni daga dukan tsoro. |
|
| 5 |
|
| Waɗanda suke dubansa sukan haskaka; fuskokinsu ba sa rufuwa da kunya. |
|
| 6 |
|
| Wannan matalauci ya yi kira, Ubangiji kuwa ya ji shi; ya cece shi daga dukan wahalarsa. |
|
| 7 |
|
| Mala’ikan Ubangiji ya kafa sansani kewaye da waɗanda suke tsoronsa, ya kuwa cece su. |
|
| 8 |
|
| Ku gwada ku gani cewa Ubangiji yana da kyau; mai albarka ne mutumin da yake neman mafaka a gare shi. |
|
| 9 |
|
| Ku ji tsoron Ubangiji, ku tsarkakansa, gama masu tsoronsa ba sa rasa kome. |
|
| 10 |
|
| Zakoki za su iya rasa ƙarfi su kuma ji yunwa, amma waɗanda suke neman Ubangiji ba sa rasa abu mai kyau. |
|
| 11 |
|
| Ku zo, ’ya’yana, ku saurare ni; zan koya muku tsoron Ubangiji. |
|
| 12 |
|
| Duk waninku da yake ƙaunar rayuwa yana kuma so yă ga kwanaki masu kyau, |
|
| 13 |
|
| ka kiyaye harshenka daga mugunta da kuma leɓunanku daga faɗar ƙarairayi. |
|
| 14 |
|
| Juyo daga mugunta ku yi alheri; nemi salama ku kuma yi ƙoƙarin samunta. |
|
| 15 |
|
| Idanun Ubangiji suna a kan masu adalci kuma kunnuwansa suna sauraran kukansu; |
|
| 16 |
|
| fuskar Ubangiji yana gāba da waɗanda suke aikata mugunta, don yă sa a manta da su a duniya. |
|
| 17 |
|
| Adalai kan yi kuka, Ubangiji kuwa yakan ji su; yakan cece su daga dukan wahalarsu. |
|
| 18 |
|
| Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu. |
|
| 19 |
|
| Adali zai iya kasance da wahala da yawa, amma Ubangiji yakan cece shi daga dukansu; |
|
| 20 |
|
| yakan tsare dukan ƙasusuwansa, ba ko ɗayansu da zai karye. |
|
| 21 |
|
| Mugunta zai kashe mugu; za a hukunta abokan gāban adalai. |
|
| 22 |
|
| Ubangiji yakan cece bayinsa; ba wanda yake neman mafaka a wurinsa da za a hukunta. |
|
|
|
|