|
| 1 |
|
| Ka yi hamayya da masu hamayya da ni, ya Ubangiji, Ka yi faɗa da masu faɗa da ni! |
|
| 2 |
|
| Ɗauki garkuwa da makamanka, ka zo ka taimake ni. |
|
| 3 |
|
| Ka daga mashin yaƙinka sama, da gatarinka, Ka yi gaba da masu fafarata. Ka faɗa mini kai ne Mai Cetona! |
|
| 4 |
|
| Ka sa a kori waɗanda suke ƙoƙari su kashe ni, a kunyatar da su! Ka sa waɗanda suke mini maƙarƙashiya su juya da baya, su ruɗe! |
|
| 5 |
|
| Ka sa su zama kamar tattakar da iska take kwashewa, Kamar waɗanda mala'ikan Ubangiji yake korarsu! |
|
| 6 |
|
| Ka sa hanyarsu ta duhunta, ta yi santsi, A sa'ad da mala'ikan Ubangiji yake fyaɗe su ƙasa! |
|
| 7 |
|
| Suka kafa mini tarko ba dalili, Sun kuma haƙa rami mai zurfi don in faɗa ciki. |
|
| 8 |
|
| Amma kafin su farga, hallaka za ta kama su. Tarkunan da suka kafa za su kama su, Su kuma fāɗa cikin ramin da suka haƙa! |
|
| 9 |
|
| Sa'an nan zan yi murna saboda Ubangiji, Zan yi murna, gama ya cece ni. |
|
| 10 |
|
| Da zuciya ɗaya zan ce wa Ubangiji, “Ba wani kamarka! Kakan kāre marasa ƙarfi daga masu ƙarfi, Talaka da matalauci kuma daga azzalumai!” |
|
| 11 |
|
| Mugaye suna ba da muguwar shaida a kaina, Suna kai ƙarata a kan laifofin da ban san kome a kansa ba. |
|
| 12 |
|
| Sun sāka mini alheri da mugunta, Cike nake da nadama. |
|
| 13 |
|
| Amma sa'ad da suke ciwo, nakan sa tufafin makoki, Na ƙi cin abinci, Na yi addu'a da kaina a sunkuye, |
|
| 14 |
|
| Kamar yadda zan yi wa aboki ko ɗan'uwa addu'a. Ina tafe a takure saboda makoki, Kamar wanda yake makoki domin mahaifiyarsa. |
|
| 15 |
|
| Sa'ad da nake shan wahala, Murna suke yi duka, Sun kewaye ni, suna ta yi mini dariya, Baƙi sun duke ni, suna ta buguna. |
|
| 16 |
|
| Suka wahalshe ni, suka yi mini dariya, Suna hararata da ƙiyayya. |
|
| 17 |
|
| Sai yaushe, za ka duba, ya Ubangiji? Ka kuɓutar da ni daga farmakinsu, Ka ceci raina daga waɗannan zakoki! |
|
| 18 |
|
| Sa'an nan zan yi maka godiya a gaban babban taron jama'a. Zan yabe ka a gaban babban taro. |
|
| 19 |
|
| Kada ka bar maƙiyana, maƙaryatan nan, su ga fāɗuwata! Kada ka bar waɗanda suke ƙina ba dalili, Su ƙyaface ni, su yi murna saboda baƙin cikina! |
|
| 20 |
|
| Ba su yin maganar zumunci, A maimakon haka sukan ƙaga ƙarairayi a kan masu ƙaunar limana. |
|
| 21 |
|
| Sukan zarge ni da kakkausan harshe, Su ce, “Mun ga abin da ka yi!” |
|
| 22 |
|
| Amma kai, ya Ubangiji ka ga wannan. Saboda haka kada ka ƙyale su, ya Ubangiji, Kada ka yi nisa! |
|
| 23 |
|
| Ka tashi, ya Ubangiji, ka kāre ni. Ya Allah ka tashi, ka bi mini hakkina. |
|
| 24 |
|
| Kai mai adalci ne, ya Ubangiji, ka shaida rashin laifina, Kada ka bar maƙiyana su ƙyaface ni, ya Allahna! |
|
| 25 |
|
| Kada ka bar su su ce wa kansu, “Madalla! Da ma abin da muke so ke nan!” Kada ka bar su su ce, “Mun rinjaye shi!” |
|
| 26 |
|
| Ka sa waɗanda suka ƙyaface ni a wahalata, A rinjaye su, su ruɗe. Ka sa waɗanda suke ɗaukar kansu sun fi ni, Su sha kunya da wulakanci! |
|
| 27 |
|
| Ka sa waɗanda suke murna da kuɓutata Su yi ta sowa ta murna, suna cewa, “Ubangiji mai girma ne! Yana murna da cin nasarar bawansa!” |
|
| 28 |
|
| Sa'an nan zan yi shelar adalcinka, Dukan yini kuwa zan yi ta yabonka. |
|
|
|
|