Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Zunubi yakan yi magana da mugun daga can gindin zuciyarsa, Yakan ƙi Allah, ba ya jin tsoronsa. |
| 2 |
| Domin yana ganin kansa shi wani abu ne, A tsammaninsa Allah ba zai tona asirinsa ba, Ya hukunta zunubinsa. |
| 3 |
| Maganarsa mugunta ce cike da ƙarairayi, Ba shi da sauran isasshiyar hikima da zai aikata nagarta. |
| 4 |
| Yana ƙulla mugunta lokacin da yake kwance a gadonsa, Halinsa ba shi da kyau, Ba ya ƙin abin da yake mugu. |
| 5 |
| Madawwamiyar ƙaunarka, ya Ubangiji, Ta kai har sammai, Amincinka ya kai sararin sammai. |
| 6 |
| Adalcinka kafaffe ne, Kamar manyan duwatsu. Hukuntanka kamar teku mai zurfi suke. Ya Ubangiji, kai kake lura da mutane da dabbobi. |
| 7 |
| Ina misalin darajar madawwamiyar ƙaunarka, ya Ubangiji! Mutane sukan sami mafaka a ƙarƙashin fikafikanka. |
| 8 |
| Sukan yi biki da yalwataccen abincin da yake Haikalinka, Kakan shayar da su daga koginka na alheri. |
| 9 |
| Kai ne mafarin dukan rai, Saboda haskenka ne kuma, muke ganin haske, |
| 10 |
| Ka yi ta ƙaunar waɗanda suka san ka, Ka yi wa adalai alheri. |
| 11 |
| Kada ka bar masu girmankai su fāɗa mini, Kada ka bar mugaye su kore ni. |
| 12 |
| Dubi inda mugaye suka fāɗi! Can suka kwanta, ba su iya tashi. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/psalms/036.mp3
150
36