Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Akwai magana a cikin zuciyata game da zunubin mugu. Babu tsoron Allah a idanunsa. |
| 2 |
| Gama a idanunsa yana ganin kansa wani abu ne wanda ya sha ƙarfi a gane ko ya ƙi zunubinsa. |
| 3 |
| Kalmomin bakinsa mugaye ne da kuma ruɗu; ya daina zama mai hikima da yin alheri. |
| 4 |
| Ko a kan gadonsa ma yana shirya mugunta; yakan sa kansa ga aikata zunubi kuma ba ya ƙin abin da ba shi da kyau. |
| 5 |
| Ƙaunarka, ya Ubangiji, kan kai sammai, amincinka har sararin sammai. |
| 6 |
| Adalcinka yana kama da manyan duwatsu, hukuncinka kamar zurfi mai girma. Ya Ubangiji, kana lura da mutum da dabba. |
| 7 |
| Ina misalin ƙaunarka marar ƙarewa! Mutane manya da ƙanana kan sami mafaka cikin inuwar fikafikanka. |
| 8 |
| Suna biki a yalwar gidanka; kakan ba su sha daga rafin farin cikinka. |
| 9 |
| Gama a gare ka akwai maɓulɓular rai cikin haskenka mukan ga haske. |
| 10 |
| Ka ci gaba da ƙaunarka ga waɗanda suka san ka, adalcinka ga masu gaskiyar zuciya. |
| 11 |
| Kada ka bari ƙafar mai girman kai yă fāɗa mini, ko hannun mugu ya kore ni. |
| 12 |
| Dubi yadda masu aikata zunubi suka fāɗi, a zube, ba za su kuwa iya tashi ba! |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/036.mp3
150
36