Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Kada ka tsorata saboda mugayen mutane ko ka yi kishin waɗanda suka aikata mugunta; |
| 2 |
| gama kamar ciyawa za su bushe, kamar ɗanyun ganyaye za su mutu. |
| 3 |
| Ka dogara ga Ubangiji ka kuma aikata alheri; yi zama cikin ƙasar ka kuma more makiyaya mai lafiya. |
| 4 |
| Ka ji daɗinka a cikin Ubangiji zai kuwa biya bukatun zuciyarka. |
| 5 |
| Ka sa kanka a hanyar Ubangiji; ka kuma dogara gare shi zai kuwa yi wannan. |
| 6 |
| Zai sa adalcinka yă haskaka kamar hasken safiya, gaskiyarka kuma kamar rana a tsaka. |
| 7 |
| Ka natsu a gaban Ubangiji ka kuma jira da haƙuri gare shi; kada ka tsorata sa’ad da mutane ke nasara a hanyoyinsu, sa’ad da suke aikata mugayen shirye-shiryensu. |
| 8 |
| Kada ka yi fushi kada kuma ka yi hasala; kada ka tsorata, wannan yakan kai ga mugunta ne kawai. |
| 9 |
| Gama za a datse mugayen mutane, amma waɗanda suke sa zuciya ga Ubangiji za su gāji ƙasar. |
| 10 |
| A ɗan ƙanƙanen lokaci, mugaye za su shuɗe; ko ka neme su, ba za a same su ba. |
| 11 |
| Amma masu tawali’u za su gāji ƙasar su kuma zauna da cikakkiyar salama. |
| 12 |
| Mugaye sukan shirya wa adalai maƙarƙashiya su ciji baki a kansu; |
| 13 |
| amma Ubangiji yakan yi dariyar mugaye, gama ya sani ranarsu tana zuwa. |
| 14 |
| Mugaye sukan zare takobi su ja baka don su kashe matalauta da masu bukata, don su kashe waɗanda hanyoyinsu daidai suke. |
| 15 |
| Amma takubansu za su soki zukatansu, kuma bakkunansu za su kakkarye. |
| 16 |
| Ƙanƙanen abin da mai adalci yake da shi ya fi arzikin mugaye yawa; |
| 17 |
| gama za a kakkarya ikon mugaye, amma Ubangiji zai riƙe mai adalci. |
| 18 |
| Kwanakin marasa zarge suna sane ga Ubangiji, kuma gādonsu zai dawwama har abada. |
| 19 |
| A lokutan masifu ba za su yanƙwane ba; a kwanakin yunwa za su sami a yalwace. |
| 20 |
| Amma mugaye za su hallaka, Abokan gāban Ubangiji za su zama kamar kyan gonaki, za su ɓace, za su ɓace kamar hayaƙi. |
| 21 |
| Mugaye kan yi rance ba sa kuma biya, amma masu adalci suna bayar hannu sake; |
| 22 |
| waɗanda Ubangiji ya sa wa albarka za su gāji ƙasar, amma waɗanda ya la’anta, za a kore su. |
| 23 |
| In Ubangiji ya ji daɗin hanyar da mutum yake bi, zai sa sawu su kahu; |
| 24 |
| ko ya yi tuntuɓe, ba zai fāɗi ba, gama Ubangiji yakan riƙe shi da hannunsa. |
| 25 |
| Dā ni yaro ne amma yanzu na tsufa, duk da haka ban taɓa ganin an yashe masu adalci ba ko a ce ’ya’yansu suna roƙon burodi. |
| 26 |
| Kullum suna bayar hannu sake suna kuma ba da bashi ba da wahala ba, za a yi wa ’ya’yansu albarka. |
| 27 |
| Ku juyo daga mugunta ku yi alheri; sa’an nan za ku zauna a ƙasar har abada. |
| 28 |
| Gama Ubangiji yana ƙaunar masu aikata daidai kuma ba zai yashe amintattunsa ba. Za a hallaka masu aikata mugunta gaba ɗaya, ’ya’yan mugaye za su hallaka. |
| 29 |
| Masu adalci za su gāji ƙasar su kuma zauna a cikinta har abada. |
| 30 |
| Bakin mutum mai adalci yakan yi magana da hikima, harshensa kuwa yakan yi maganar abin da yake daidai. |
| 31 |
| Dokar Allahnsa tana a cikin zuciyarsa; ƙafafunsa ba sa santsi. |
| 32 |
| Mugaye suna fako suna jira masu adalci, suna ƙoƙari neman ransu; |
| 33 |
| amma Ubangiji ba zai bar su a ikonsu ba ko ya bari a hukunta su sa’ad da aka kawo su shari’a ba. |
| 34 |
| Ku sa zuciya ga Ubangiji ku kuma kiyaye hanyarsa. Zai ɗaukaka ku ku ci gādon ƙasar, sa’ad da aka kawar da mugaye, za ka gani. |
| 35 |
| Na ga wani mugu, azzalumi, yana yaɗuwa kamar ɗanyen itace a asalin ƙasarsa, |
| 36 |
| amma yakan mutu nan da nan kuma ba ya ƙara kasancewa; ko an neme shi, ba za a same shi ba. |
| 37 |
| Ka dubi marasa zargi, ka lura da adali; akwai sa zuciya domin mutum mai salama. |
| 38 |
| Amma za a hallaka dukan masu zunubi; za a yanke sa zuciya ta mugaye. |
| 39 |
| Ceton adalai kan zo daga Ubangiji; shi ne mafaka a lokacin wahala. |
| 40 |
| Ubangiji yakan taimake su yă kuma cece su; yakan kuɓutar da su daga mugaye yă kuma cece su, domin sukan nemi mafaka daga gare shi. |
|
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/037.mp3
150
37