Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Mai albarka ne wanda yake jin tausayin marasa ƙarfi; Ubangiji yakan kuɓutar da shi a lokutan wahala. |
| 2 |
| Ubangiji zai kāre shi yă kuma kiyaye ransa; zai albarkace shi a cikin ƙasar ba kuwa zai miƙa shi ga hannun maƙiyansa ba. |
| 3 |
| Ubangiji zai ba shi ƙarfi a gadon rashin lafiyarsa ya mayar masa da lafiya daga ciwon da ya kwantar da shi. |
| 4 |
| Na ce, “Ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai; ka warkar da ni, gama na yi maka zunubi.” |
| 5 |
| Abokan gābana suna muguwar magana a kaina cewa, “Yaushe zai mutu sunansa yă ɓace ne?” |
| 6 |
| Duk sa’ad da wani ya zo ganina, yakan yi maganar ƙarya, yayinda zuciyarsa tana tattare da cin zarafi; sa’an nan yă fita yă yi ta bazawa ko’ina. |
| 7 |
| Dukan abokan gābana suna raɗa tare a kaina; suna fata mugun abu ya same ni, suna cewa, |
| 8 |
| “Mugun ciwo ya kama shi; ba zai taɓa tashi daga inda yake kwanciya ba.” |
| 9 |
| Har abokina na kurkusa, wanda na amince da shi, wanda muke cin abinci tare, ya juya yana gāba da ni. |
| 10 |
| Amma kai, ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai, ka tā da ni, don in sāka musu. |
| 11 |
| Na sani kana jin daɗina, gama abokin gābana ba zai ci nasara a kaina ba. |
| 12 |
| Cikin mutuncina ka riƙe ni ka sa ni a gabanka har abada. |
| 13 |
| Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, har abada abadin. Amin kuma Amin. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/041.mp3
150
41