Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ku tafa hannuwanku, dukanku al’ummai; ku yi sowa ga Allah da muryoyin farin ciki. |
| 2 |
| Ubangiji Mafi Ɗaukaka mai banmamaki ne, Sarki ne mai girma a bisa dukan duniya! |
| 3 |
| Ya rinjayi al’ummai a ƙarƙashinmu, mutane kuma a ƙarƙashin ƙafafunmu. |
| 4 |
| Ya zaɓar mana gādonmu, abar taƙamar Yaƙub, wanda yake ƙauna. |
| 5 |
| Allah ya haura a cikin sowa ta farin ciki, Ubangiji ya haura a cikin ƙarar ƙahoni. |
| 6 |
| Ku rera yabai ga Allah, ku rera yabai; ku rera yabai ga Sarkinmu, ku rera yabai. |
| 7 |
| Gama Allah shi ne Sarkin dukan duniya; ku rera zabura ta yabo gare shi. |
| 8 |
| Allah yana mulki a bisa al’ummai; Allah yana zama a kan kursiyinsa mai tsarki. |
| 9 |
| Manyan mutanen al’ummai sun taru a matsayin mutanen Allah na Ibrahim, gama sarkunan duniya na Allah ne; ana ɗaukaka shi ƙwarai. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/047.mp3
150
47