Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Ubangiji mai girma ne, Dole kuwa a yabe shi da girmamawa a birnin Allahnmu, A kan tsattsarkan dutsensa. |
| 2 |
| Dutsen Sihiyona, dutse mai tsawo, Mai kyan gani ne na Allah, Birnin babban Sarki. Yakan kawo farin ciki ga dukan duniya! |
| 3 |
| Allah ya nuna akwai zaman lafiya a wurinsa, A kagarar birnin. |
| 4 |
| Sarakuna suka tattaru, Suka zo Dutsen Sihiyona, |
| 5 |
| Da suka gan shi sai suka yi mamaki, Suka tsorata suka gudu. |
| 6 |
| Tsoro ya kama su suka razana, Kamar mace wadda take gab da haihuwa. |
| 7 |
| Allah yakan hallaka manyan jiragen ruwa da iskar gabas. |
| 8 |
| Mun ji labarin waɗannan al'amura, Yanzu kuwa mun gan su A birnin Allahnmu, Mai Runduna, Zai kiyaye birnin lafiya har abada. |
| 9 |
| A cikin Haikalinka, ya Allah, Muna tunanin madawwamiyar ƙaunarka. |
| 10 |
| A ko'ina jama'a suna yabonka, Sunanka ya game duniya duka. Kana mulki da adalci. |
| 11 |
| Bari jama'ar Sihiyona su yi murna! Gama kana shari'a ta gaskiya, Bari biranen Yahuza su yi farin ciki. |
| 12 |
| Ku tafi ku kewaye Dutsen Sihiyona, Ku ƙirga yawan hasumiyarsa. |
| 13 |
| Ku lura da garukanta, ku bincike kagaranta, Saboda ku iya faɗa wa tsara mai zuwa, |
| 14 |
| Cewa wannan Allah shi ne Allahnmu har abada abadin, Shi ne zai bishe mu a dukan zamanai masu zuwa. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/psalms/048.mp3
150
48