Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ubangiji mai girma ne, kuma mafificin yabo, a birnin Allahnmu, dutsensa mai tsarki. |
| 2 |
| Kyakkyawa ce cikin tsayinta, abin farin cikin dukan duniya. Kamar ƙwanƙoli mafi tsayi na Zafon ne Dutsen Sihiyona, birnin Babban Sarki. |
| 3 |
| Allah yana cikin fadodinta; ya nuna kansa mafaka ce gare ta. |
| 4 |
| Sa’ad da sarakuna suka haɗa rundunoni, sa’ad da suka yi gaba tare, |
| 5 |
| sun gan ta suka kuwa yi mamaki; suka gudu don tsoro. |
| 6 |
| Rawar jiki ya kama su a can, zafi kamar na mace mai naƙuda. |
| 7 |
| Ka hallaka su kamar jiragen ruwan Tarshish da iskar gabas ta wargaje. |
| 8 |
| Yadda muka ji, haka muka gani a cikin birnin Ubangiji Maɗaukaki, a cikin birnin Allahnmu. Allah ya sa ta zauna lafiya har abada. |
| 9 |
| Cikin haikalinka, ya Allah, mun yi tunani a kan ƙaunarka marar ƙarewa. |
| 10 |
| Kamar sunanka, ya Allah, yabonka ya kai iyakokin duniya; hannunka na dama ya cika da adalci. |
| 11 |
| Dutsen Sihiyona ya yi farin ciki, ƙauyukan Yahuda suna murna saboda hukuntanka. |
| 12 |
| Yi tafiya cikin Sihiyona, ku kewaye ta, ku ƙirga hasumiyoyinta, |
| 13 |
| ku lura da katangarta da kyau, ku dubi fadodinta, don ku faɗe su ga tsara mai zuwa. |
| 14 |
| Gama wannan Allah shi ne Allahnmu har abada abadin; zai zama jagorarmu har zuwa ƙarshe. |
|
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/048.mp3
150
48