Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ka saurare kalmomina, ya Ubangiji, ka ji ajiyar zuciyata. |
| 2 |
| Ka saurare kukata na neman taimako, Sarkina da Allahna, gama gare ka nake addu’a. |
| 3 |
| Da safe, ya Ubangiji, ka ji muryata; da safe na gabatar da bukatuna a gabanka in kuma jira da sa zuciya. |
| 4 |
| Kai ba Allahn da yake jin daɗin mugu ba ne; gama kana gāba da dukan masu aikata mugunta. |
| 5 |
| Masu fariya ba za su iya tsaya a gabanka ba. Kana ƙin duk masu aikata abin da ba daidai ba. |
| 6 |
| Kakan hallaka masu yin ƙarya. Masu kisankai da mutane masu ruɗu Ubangiji yana ƙyama. |
| 7 |
| Amma ni, ta wurin jinƙanka mai girma, zan shiga gidanka; da bangirma zan durƙusa ga haikalinka. |
| 8 |
| Ka bi da ni, ya Ubangiji, cikin adalcinka saboda abokan gābana, ka fayyace hanyarka a gabana. |
| 9 |
| Babu ko kalma guda daga bakinsu da za a dogara da ita; marmarinsu kawai shi ne su hallakar da waɗansu. Maƙogwaronsu buɗaɗɗen kabari ne; da harshensu suna faɗin ƙarya. |
| 10 |
| Ka furta su masu laifi, ya Allah! Bari makircinsu yă zama fāɗuwarsu. Ka kore su saboda yawan zunubansu, saboda sun tayar maka. |
| 11 |
| Amma bari dukan waɗanda suke neman mafaka gare ka su yi murna; bari kullum su yi ta rerawa saboda farin ciki. Ka buɗe kāriyarka a bisansu, domin waɗanda suke ƙaunar sunanka su yi farin ciki a cikinka. |
| 12 |
| Gama tabbatacce, ya Ubangiji, kakan albarkaci adalai; kakan kewaye su da tagomashinka kamar garkuwa. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/005.mp3
150
5