|
| 1 |
|
| Maɗaukaki, Allah, Ubangiji, ya yi magana ya kuma kira duniya daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa. |
|
| 2 |
|
| Daga Sihiyona, cikakkiya a kyau, Allah na haskakawa. |
|
| 3 |
|
| Allahnmu yana zuwa ba kuwa zai yi shiru ba; wuta mai cinyewa a gabansa, babban hadari kuma ya kewaye shi. |
|
| 4 |
|
| Ya kira sammai da suke bisa, da duniya, don yă shari’anta mutanensa. |
|
| 5 |
|
| “Ku tattara mini shafaffuna, waɗanda suka yi alkawari da ni ta wurin hadaya.” |
|
| 6 |
|
| Sammai kuwa sun yi shelar adalcinsa gama Allah kansa alƙali ne. |
|
| 7 |
|
| “Ku ji, ya mutanena, zan kuwa yi magana, Ya Isra’ila, zan kuwa ba da shaida a kanku. Ni ne Allah, Allahnku. |
|
| 8 |
|
| Ba na tsawata muku saboda hadayunku ko kuwa hadayunku na ƙonawa, waɗanda kuka taɓa kawo a gabana. |
|
| 9 |
|
| Ba na bukatan bijimi daga turkenku ko awaki daga garkunanku, |
|
| 10 |
|
| gama kowace dabbar kurmi nawa ne, da kuma shanu a kan dubban tuddai. |
|
| 11 |
|
| Na san kowane tsuntsun da yake a duwatsu kuma halittun filaye nawa ne. |
|
| 12 |
|
| Da a ce ina jin yunwa ai, ba sai na faɗa muku ba, gama duniyar nawa ne, da kome da yake cikinta. |
|
| 13 |
|
| Ina cin naman bijimai ne ko ina shan jinin awaki ne? |
|
| 14 |
|
| “Ku miƙa hadayar godiya ga Allah, ku cika alkawuranku ga Mafi Ɗaukaka, |
|
| 15 |
|
| ku kira gare ni a ranar wahala; zan cece ku, za ku kuwa girmama ni.” |
|
| 16 |
|
| Amma ga mugaye, Allah ya ce, “Wace dama ce kuke da ita na haddace dokokina ko na yin maganar alkawarina a leɓunanku? |
|
| 17 |
|
| Kun ƙi umarnina kuka kuma zubar da kalmomina a bayanku |
|
| 18 |
|
| Sa’ad da kuka ga ɓarawo, kukan haɗa kai da shi; kukan haɗa kai da mazinata. |
|
| 19 |
|
| Kuna amfani da bakunanku don mugunta kuna kuma gyara harshenku don ruɗu. |
|
| 20 |
|
| Kuna ci gaba da magana a kan ɗan’uwanku ku kuma yi maganar ƙarya a kan ɗan mahaifinku. |
|
| 21 |
|
| Kun yi waɗannan abubuwa na kuwa yi shiru; kun ɗauka gaba ɗaya ni kamar ku ne. Amma zan tsawata muku in kuma zarge ku a fuskarku. |
|
| 22 |
|
| “Ku lura da wannan, ku da kuka manta da Allah, ko kuwa in yayyage ku kucu-kucu, ba kuma wanda zai cece ku. |
|
| 23 |
|
| Shi wanda ya miƙa hadayun godiya yakan girmama ni, ya kuma shirya hanya saboda in nuna masa ceton Allah.” |
|
|
|
|