Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Wawa ne kawai yakan ce a zuciyarsa, “Ba Allah.” Sun lalace, kuma hanyoyinsu ba su da kyau; babu wani mai aikata abu mai kyau. |
| 2 |
| Allah yana duba daga sama a kan ’ya’yan mutane yă ga ko akwai wani wanda ya gane, wani wanda yake neman Allah. |
| 3 |
| Kowa ya kauce, gaba ɗaya sun lalace; babu guda da yake aikata abu mai kyau, babu ko ɗaya. |
| 4 |
| Masu aikata mugunta ba sa taɓa koyo? Suna cin mutanena kamar yadda ake cin burodi, ba sa kuma kira ga Allah. |
| 5 |
| Ga shi fa, sun firgita don tsoro, ko da yake babu dalilin tsoro, gama Allah zai watsar da ƙasusuwan masu ƙinsa, za su sha kunya, gama Allah ya ƙi su. |
| 6 |
| Kash, da ceton Isra’ila zai fito daga Sihiyona mana! Sa’ad da Allah ya sāke arzuta mutanensa, bari Yaƙub yă yi farin ciki Isra’ila kuma yă yi murna! |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/053.mp3
150
53