Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Ka cece ni ta wurin ikonka, ya Allah, Ka cece ni ta wurin ƙarfinka! |
| 2 |
| Ka ji addu'ata, ya Allah, Ka saurari kalmomina! |
| 3 |
| Masu girmankai sun tasar mini, Mugaye suna nema su kashe ni, Mutanen da ba su kula da Allah ba. |
| 4 |
| Na sani Allah ne mai taimakona, Na sani Ubangiji shi ne mai tsarona! |
| 5 |
| Ubangiji ya hukunta wa maƙiyana da irin muguntarsu! Gama zai hallaka su saboda shi mai aminci ne. |
| 6 |
| Da murna zan miƙa maka hadaya, Zan yi maka godiya, ya Ubangiji, Domin kai mai alheri ne. |
| 7 |
| Ka cece ni daga dukan wahalaina, Na kuwa ga an kori maƙiyana. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/psalms/054.mp3
150
54