Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Ka yi mini jinƙai, ya Allah, Gama mutane sun tasar mini, Maƙiyana suna tsananta mini koyaushe! |
| 2 |
| Dukan yini maƙiyana suna tasar mini, Waɗanda suke faɗa da ni sun cika yawa. |
| 3 |
| Sa'ad da nake jin tsoro, ya Maɗaukaki, A gare ka nake dogara. |
| 4 |
| Ga Allah nake dogara, ina yabon alkawarinsa, Gare shi na dogara, ba zan ji tsoro ba. Me mutum kawai zai yi mini? |
| 5 |
| Maƙiyana suke ta wahalshe ni dukan yini, A kan kowane abu da nake yi, Kullum suna ta tunanin yadda za su cuce ni! |
| 6 |
| Sukan taru a ɓoye, Suna kallon duk abin da nake yi. Suna sa zuciya za su iya kashe ni. |
| 7 |
| Ka hukunta su, ya Allah saboda muguntarsu, Da fushinka ka kori waɗannan mutane! |
| 8 |
| Ka san irin wahalar da nake sha, Kana riƙe da lissafin yawan hawayena. Ashe, ba a rubuce suke a littafinka ba? |
| 9 |
| A ranar da na yi kira gare ka, Za a komar da abokan gābana baya, Gama na sani Allah yana tare da ni! |
| 10 |
| Ina dogara ga Allah, ina yabon alkawarinsa, Ina dogara ga Ubangiji, ina yabon alkawarinsa. |
| 11 |
| A gare shi nake dogara, Ba zan ji tsoro ba. Me mutum kawai zai yi mini? |
| 12 |
| Zan miƙa maka abin da na yi alkawari, ya Allah, Zan miƙa maka hadaya ta godiya. |
| 13 |
| Domin ka cece ni daga mutuwa, Ka hana a ci nasara a kaina. Saboda haka a gaban Allah nake tafiya A hasken da yake haskaka wa masu rai. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/psalms/056.mp3
150
56