Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ka yi mini jinƙai, ya Allah, gama mutane sun tasar mini da zafi; dukan yini suna matsa harinsu. |
| 2 |
| Masu ɓata sunana suna bina dukan yini; da yawa suna kai mini hari cikin fariyarsu. |
| 3 |
| Sa’ad da nake tsoro, zan dogara gare ka. |
| 4 |
| Ga Allah wanda maganarsa nake yabo ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba. Me mutum mai mutuwa zai yi mini? |
| 5 |
| Dukan yini sun yi ta juya maganata; kullum suna ƙulle-ƙulle su cuce ni. |
| 6 |
| Sun haɗa baki, sun ɓoye, suna kallon takawata suna a shirye su ɗauki raina. |
| 7 |
| Sam, kada ka bari su kuɓuce; cikin fushinka, ya Allah, ka saukar da al’ummai. |
| 8 |
| Ka lissafta makokina; ka jera hawayena a littafinka, ba a rubuce suke a cikin littafinka ba? |
| 9 |
| Ta haka abokan gābana za su juya da baya sa’ad da na nemi taimako. Ta haka zan san cewa Allah yana tare da ni. |
| 10 |
| Ga Allah, wanda nake yabon maganarsa, ga Ubangiji, wanda nake yabon maganarsa, |
| 11 |
| ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai iya yi mini? |
| 12 |
| Ina ƙarƙashin alkawari gare ka, ya Allah; zan miƙa hadayuna na godiya gare ka. |
| 13 |
| Gama ka cece ni daga mutuwa da kuma ƙafafun daga tuntuɓe, don in yi tafiya a gaban Allah cikin hasken rai. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/056.mp3
150
56