Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Hakika za ku yanka daidai, ku manya? Za ku shara'anta wa mutane daidai? |
| 2 |
| A'a, tunanin muguntar da za ku aikata kaɗai kuke yi, Kuna aikata laifofin ta da hargitsi a ƙasar. |
| 3 |
| Mugaye, laifi suke yi dukan kwanakinsu, Tun daga ranar da aka haife su suke ta faɗar ƙarya. |
| 4 |
| Cike suke da dafi kamar macizai, Sukan toshe kunnuwansu kamar kuraman gamsheƙa, |
| 5 |
| Wanda ba ya jin muryar gardi, Ko kuma waƙar gwanin sihiri. |
| 6 |
| Ka kakkarya haƙoransu, ya Allah, Ka ciccire fiƙoƙin waɗannan zakoki masu zafin rai, ya Ubangiji! |
| 7 |
| Bari su ɓace kamar ruwan da ya tsanye, Bari a murtsuke su kamar ciyayi a hanya. |
| 8 |
| Bari su zama kamar katantanwu waɗanda sukan narke su yi yauƙi, Allah ya sa su zama kamar jinjirin da aka haifa matacce. Wanda bai taɓa ganin hasken rana ba. |
| 9 |
| Kafin tukunya ta ji zafin wuta, Da zafin fushi, Allah zai watsar da su tun suna da rai. |
| 10 |
| Adalai za su yi murna sa'ad da suka ga an hukunta masu zunubi, Za su wanke ƙafafunsu cikin jinin mugaye. |
| 11 |
| Mutane za su ce, “Hakika an sāka wa adalai, Hakika akwai Allah wanda yake shara'anta duniya!” |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/psalms/058.mp3
150
58