Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ku masu mulki tabbatacce kuna magana daidai? Kuna yin shari’a daidai a cikin mutane? |
| 2 |
| Sam, a zuciyarku kuna ƙirƙiro rashin adalci, da hannuwanku kuma kuna tā da hargitsi a duniya. |
| 3 |
| Kai, tun haihuwa mugaye sukan kauce; daga cikin ciki, su lalatattu ne maƙaryata. |
| 4 |
| Dafinsu ya yi kamar dafin maciji, kamar na gamsheƙan da ya toshe kunnuwansa, |
| 5 |
| da ba ya jin muryar gardi, kome dabarar gwanin mai waƙar zai zama. |
| 6 |
| Ka kakkarya haƙoran a bakunansu, ya Allah; ka yayyage fiƙoƙin zakoki, ya Ubangiji! |
| 7 |
| Bari su ɓace kamar ruwa mai wucewa; sa’ad da suka ja bakansu, bari kibiyoyinsu su murtsuke. |
| 8 |
| Kamar katantanwun da suke narkewa yayinda suke tafiya, kamar jinjirin da aka haifa matacce, kada su ga hasken rana. |
| 9 |
| Kafin tukwanenka su ji zafin ƙayayyuwa, ko su kore ne ko busasshe, za a shafe mugaye. |
| 10 |
| Masu adalci za su yi murna sa’ad da aka rama musu, sa’ad da suka wanke ƙafafunsu cikin jinin mugaye. |
| 11 |
| Sa’an nan mutane za su ce, “Tabbatacce har yanzu ana sāka wa adalai; tabbatacce akwai Allahn da yake shari’anta duniya.” |
|
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/058.mp3
150
58