Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ka cece ni daga abokan gābana, ya Allah; ka tsare ni daga waɗanda suka tayar mini. |
| 2 |
| Ka kuɓutar da ni daga masu aikata mugunta ka kuma cece ni daga masu kisa. |
| 3 |
| Duba yadda suka kwanta suna jirana! Mugaye suna ƙulle-ƙullen gāba da ni ba saboda wani dalili ko na yi wa wani zunubi ba, ya Ubangiji. |
| 4 |
| Ban yi wani laifi ba, duk da haka suna a shirye su fāɗa mini. Tashi ka taimake ni; dubi halin da nake ciki! |
| 5 |
| Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, ka tashi ka hukunta dukan al’ummai; kada ka nuna jinƙai ga mugaye maciya amana. |
| 6 |
| Sukan dawo da yamma, suna wage haƙora kamar karnuka, suna yawo a birni. |
| 7 |
| Dubi abin da suke tofawa daga bakunansu, suna tofar da takuba daga leɓunansu, suna cewa, “Wa zai ji mu?” |
| 8 |
| Amma kai, ya Ubangiji, kakan yi musu dariya; kana yi wa dukan waɗannan al’ummai ba’a. |
| 9 |
| Ya ƙarfina, na dogara gare ka; kai, ya Allah, kai ne kagarata, |
| 10 |
| Allah mai ƙaunata. Allah zai sha gabana zai kuma sa in yi dariya a kan waɗanda suke magana marar kyau a kaina. |
| 11 |
| Amma kada ka kashe su, ya Ubangiji garkuwarmu, in ba haka mutanena za su manta. Cikin ikonka ka sa su yi ta yawo barkatai, ka kuma kawar da su. |
| 12 |
| Saboda zunuban bakunansu, saboda maganganun leɓunansu, bari a kama su cikin fariyarsu. Saboda zage-zage da ƙarairayin da suke yi, |
| 13 |
| ka cinye su da hasala, ka cinye su sarai. Sa’an nan za a sani a iyakar duniya cewa Allah yana mulki a bisa Yaƙub. |
| 14 |
| Sukan dawo da yamma, suna wage haƙora kamar karnuka, suna yawo a birni. |
| 15 |
| Suna ta yawo neman abinci su kuwa yi haushi in ba su ƙoshi ba. |
| 16 |
| Amma zan rera game da ƙarfinka, da safe zan rera game da ƙaunarka; gama kai ne mafakata, kagarata a lokacin wahala. |
| 17 |
| Ya ƙarfina, na rera yabo gare ka; kai, ya Allah, kai ne kagarata, Allah mai ƙaunata. |
|
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/059.mp3
150
59