Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ya Ubangiji, kada ka tsawata mini cikin fushinka ko ka hore ni cikin hasalarka. |
| 2 |
| Ka yi mini jinƙai, Ubangiji, gama na suma; Ya Ubangiji, ka warkar da ni, gama ƙasusuwana suna zafin ciwo. |
| 3 |
| Raina yana cikin wahala. Har yaushe, ya Ubangiji, har yaushe? |
| 4 |
| Ka juyo, ya Ubangiji, ka cece ni; ka cece ni saboda madawwamiyar ƙaunarka. |
| 5 |
| Babu wanda yakan tuna da kai sa’ad da ya mutu. Wa ke yabonka daga kabari? |
| 6 |
| Na gaji tiƙis daga nishi. Dukan dare na jiƙe gadona da kuka na jiƙe kujerata da hawaye. |
| 7 |
| Idanuna sun rasa ƙarfi da baƙin ciki; sun rasa ƙarfi saboda dukan abokan gābana. |
| 8 |
| Ku tafi daga gare ni, dukanku masu aikata mugunta, gama Ubangiji ya ji kukata. |
| 9 |
| Ubangiji ya ji kukata saboda jinƙansa; Ubangiji ya karɓi addu’ata. |
| 10 |
| Dukan abokan gābana za su sha kunya su kuma karaya; za su juya da kunya nan da nan. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/006.mp3
150
6