Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ya Allah, kai ne Allahna, da nacewa na neme ka; raina yana ƙishinka, jikina yana marmarinka, cikin busasshiyar ƙasar da ta zozaye inda babu ruwa. |
| 2 |
| Na gan ka a wuri mai tsarki na kuma dubi ikonka da ɗaukakarka. |
| 3 |
| Domin ƙaunarka ta fi rai kyau, leɓunana za su ɗaukaka ka. |
| 4 |
| Zan yabe ka muddin raina, kuma a cikin sunanka zai ɗaga hannuwana. |
| 5 |
| Raina zai ƙoshi kamar da abinci mafi kyau; da leɓunan rerawa bakina zai yabe ka. |
| 6 |
| A gadona na tuna da kai; ina tunaninka dukan dare. |
| 7 |
| Domin kai ne mai taimakona, ina rera a cikin inuwar fikafikanka. |
| 8 |
| Raina ya manne maka; hannunka na dama yana riƙe da ni. |
| 9 |
| Su da suke neman raina za su hallaka; za su gangara zuwa zurfafan duniya. |
| 10 |
| Za a bayar da su ga takobi su kuma zama abincin karnukan jeji. |
| 11 |
| Amma sarki zai yi farin ciki ga Allah; dukan waɗanda suke rantse da sunan Allah za su yabe shi, amma za a rufe bakunan maƙaryata. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/063.mp3
150
63